Skip to content
Home » Magungunan Musulunci: Magunguna 5 da ya Kamata su Kasance Tare da Kai a Kullun

Magungunan Musulunci: Magunguna 5 da ya Kamata su Kasance Tare da Kai a Kullun

Magaungunan musulunciu suna taka muhimmiyar rawa sosai fiye da na yurawa wanda kusan sunfi warkarwa daga cututtukan da ya shafi jiki, lalura ko kuma ciwon aljannu, na mayu da sauransu.

Ba kasafai kullun ya kasance a gida baka aje maganin musulunci ba, wannan ba dabi’a bace ana son kullun ya zamani kana aje su saboda halin kwatsam abunda zai faru a cikin gida musamman lokacin dare wanda zuwa asibiti ke wahala.

A wannan post din inshallahu zamu kawo wasudaga cikin muhimman magunguna biyar wanda ya kamata ace kullun kana tare da su wanda suke kamar antibiotics a matsayin kariya daga cututtukan da suka shafi jiki ko kuma fata.

Magaungunan Musulunci Masu Mahimmanci

A cikin magunguna bakidaya idan aka yi magana akwai wadanda an ambacesu a Qur’ani mai girma kuma a hadisai da kissoshi yazo manzon Allah S.A.W yayi magana akansu misali kamar zuma wadda ba karamin magani bace kuma har sura ke akwai a kanta a cikin Qur’ani mai girma.

Amfanin Zuma baya kididiguwa wqanda a baya munyi magana akan wasu muhimman magunguna da take ga wadanda suke yawan binmun a wannan shafin, ita da sauran magunguna zamu zayyana su tare tsokaci kadan akan amfanin wasu daga cikinsu.

magungunan muslunci ga marasa lafiya

Wanda muhimman magungunan gasu kamar haka:-

  • Zuma
  • Habbatus Sauda
  • Zaitun
  • Dabino
  • Tafarnuwa

Zuma

Zuma abu ce babba wadda take magance cututtuka da dama a cikin jikin mutum kuma Allah kadai ya san iya yawan cutar da take magancewa.

An ambace ta a cikin littafi mai girma Al Qur’ani kuma ma sura daya ce kacokam wadda ake kira da suratun nahli wadda akayi magana akanta.

Zuma babban frigakafi ce wadda ya kamata ka rika ajewa a gida a koda yaushe musamman a yanayin da aka santa tana magance ciwon ciki cikin ikon Allah.

Daya daga cikin maganin da take yi shine maganin ciwon ciki wanda indai ciki yana ciwo ko kuma ya kumbura cikin ikon Allah ana samun sauki.

Sai kuma fannin abunda ya shafi makokwaro kamar cututtuka irin na Tari da Mura wanda yake kama mutane baya ga maganini abubuwan da ya shafi fata da take yi kana iya duba bayanin da mukayi a baya akan amfanin zuma.

Karanta: Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam

Habbatus Sauda

Habbatus Sauda a Turance ana kiranta da Black seed abuce mai matukat amfani itama kuma kamar anti biotics ce a cikin jikin mutum tana magance cututtuka da dama da suka shafi kirji idan aka hada ta da nono mai kyau na shanu ba wanda ya lalace ba.

Habbatus sauda abu ce mi kyau kuma ko hakanan ana son ka rika shanta da zuma kana hadawa suna taimakama lafiyar jikin dan Adam da sa shi kuzari.

Kuma a fannin ciwon ulcer ma habbatus sauda tana taka muhimmiyar rawa wajen magance ta kamar yadda mukayi magana a fannin maganin ulcer

hayakinta a cikin gida yana maganin aljannu shaidanu yana korar su daga cikin gida da izinin Allah.

Karanta: 

Yadda zaka magance gyanbon ciki ulcer Babba da karama

Maganin Ulcer da tayi Yawa(chronic) har abada

Zaitun

Zaitun magani ne na musulunci shima wanda yana yin magunguna sosai a cikin jiki kuma manshima yana magunguna fata da yawa.

man zaitun ana sama ciwo wanda ake son yayi saurin kamewa bayan ya warke ake son kada yayi tabo sosai to ana samashi zaitun cikin ikon Allah ba zai yi tabo babba yadda za’a rika ganewa ba sosai.

Bugu da kari kuma masu son karin gashi ko kuma girman gashi ko kuma tsawon gashi cikin sati daya ko kuma abunda ya wuce haka zaitun yana taimakawa gashi wajen sashi tsawo da kuma sulbi kamar a baya munyi bayani akan tsawon gashi.

karanta:

Abubuwa guda 5 dake sa tsawon gashi

Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

Dabino

Dabino abunci ne kuma yana da matukar amfani aje sa a gida saboda yadda yake taka rawa wajen gyaran ciki idan kamar kana tunanin cikinka yana neman ya lalace kana gyatsa marar dadi cin dabino yana taimakawa sosai.

Kuma bayan haihuwar jariri kamar yadda ya tabbata a kissa ana son arika tauna ma yara jarirai dabino a bakisu bayan anyi masu kiran salla saboda yadda yake da matukar amfani ga mutum

Tafarnuwa

tafarnuwa abu ce mai kyau wadda tana daga cikin na’ukan kayan sanyi ana son ajiyar tafarnuwa a gida ytana taimakawa wajen magance abubuwan da ya shafi aljannu domin basu sonta.

Kuma wani abun amfani dangane da ita shine a gida idan kana son ka kori tsaka kayi mata kisan farat daya to kasamu tafarnuwa da gishiri.

Yadda ake hada abun shine bayan ka samu tafarnuwa da gishiri ka daddaka tafarnuwar sai ka sa gishiri kabi duk wata kona ko sakon da kake tuananin tsaka da ma inda kake tunanin zata iya zuwa kasa.

bayan wani lokaci da ta zo ta shinshina wannan hadin sai dai ka tarar da gawar ta da izinin Allah.

Kammalawa

kamar dai yadda na fadi a farko yana da kyau mutum ya rika adana abubuwan ko magungunan musulunci da zasu zamar masa kamar kariya saboda ko takwana kuma mun zayyana wasu muhimman abubuwa daga cikinsu.

Saboda ba’a san abunda gobe ko anjima zata yi ba, ga mai tambaya ko neman karin bayani yana iya yi a commen section mungode.

Karanta: 

Amfanin Ruwa Dumi 5 ga Lafiyar Jiki

Maganin Ciwon Sickler da Kuma Bayani akan Cutar

Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga