Skip to content
Home » Ciwon Sickler: Maganin Ciwon Sickler da Kuma Bayani akan Cutar

Ciwon Sickler: Maganin Ciwon Sickler da Kuma Bayani akan Cutar

Ciwon Sickler ciwo ne wanda muatne da yawa suke fama da shi afadin africa musamman a kasashe irinsu Nigeria, India da kuma wasu sassa na kasar Ameriaca.

Ciwo ne wanda ba yaduwa yake ba a zahiri, anaa samun sa ne ta hanyar gado daga iyaye wanda idan daya daga cikinsu carrier ne.

Inshallahu a wannan post din zamu yi bayani akan cutar, maganin gargajiyar ciwon siclker da kuma wasu abubuwan da mai cutar ya kamata ua kula da su a fannin kiwon lafiya.

maganin ciwon sickler

Minene Ciwon Sickler

Ciwon sickler cuta ce wadda take samuwa a dalilin wasu kwayoyin halitta na cikin jini wanda ake kira da red blod cells suke canza yanayi daga zagaye kamar kwano zuwa shape ko yanayi kamar lauje.

Su wadannan red blood cells din sune suke daukar numfashin oxygen idan atsakiyar inda suke zagaye ta hanyar wani abu da ake kira da haemoglodin, idan jini ya zagaya a hunhu sai su dauki iskan oxygen su raba ma jiki.#

To a dalilin wannan matsala ta sickler wasu daga cikin cells dinn sun koma kamar lauje basu iya dauka sosai, kuma wani lokacin ma sai su riaka toshe hanyoyin jini su cunkushe a gaba wanda hakan yake hadasa ciwo a wajen gabar.

Gabobin da suke ciwo

Mai fama da wannan cutar zakaga yana cewa wasu daga cikin gabobinsa suna ciwo wanda zamu lissafa su kamar haka:-

 • Ciwon kai
 • Ciwon ciki
 • Ciwon Baya
 • Ciwon kafa
 • Ciwon Hannu
 • Ciwon Kirji

da sauransu kusan duk yawanci gabobin inda kashi yake yana yin ciwo wanda wasu kamar yara ma kusan idan ciwo yayi yawa gabar kashi kusan harma fara karyewa kadan take saboda zingar ciwo.

Abubuwan da ke Tada Ciwon

Duk da babu wani sahihin abu daya da za’a ce shine kawai zalla yake tada ta amma akwai su wanda kusan kowanensu yana iya tada cutar wanda gasu kamara haka.

 • yanayin sanyi ko kuma zafi sosai ba’a spo yayi ma masu cutar yawa
 • Yawan tashin hankali
 • Rashin ruwan jiki sosai
 • Jin ciwo sosai wanda yake haddasa zubar jini

Karanta: 

Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara

Hanyoyi 5 Masu Amfani Domin Magance Hawan jini

Maganinsa

Akwai maganin gargajiya da ake ba masu ciwon sickler wanda cikin ikon Allah ana samun sauki, yadda ake hada shi kuma shine za’a samu Zaitun mai kyau, sai a samu Nonon shanmo mai kyau ba mai tsami ba.

Bayan an samu wadannan abubuwan sai a rika sa zaitun digo ba da yawa ba kamar rabin ma tea spoon kar ya kai a rika sawa a cikin nonon shanun ana ba marar lafiyar yana sha.

Cikin ikon Allah ana samun saukin cutar idan ana fama da ita.

Karanta:

 Amfanin Yawan Shan Ruwa 6 ga Lafiya da Yakamata a Sani

Illolin da Ruwan Sanyi yake da Su a Jikin Mutum

Hanyoyin Kulawa ga mai Cutar

sauran hanyoyin da kuma abubuwan da zasu taimnaka ma mai cutar sun hada

 • yawan shan ruwa
 • Motsa jiki kada
 • Shan folic acid kamar daya a kullun da duk wani nauin abincin da zai bada folic acid
 • Karin jini idan abun yayi yawa
 • rashin zama cikin bacin rai
 •  kare ma yanayi mai tsanin kamar tsananin zafi ko kuma sanyi zama a waje madaidaici

Karanta: Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga

Tags: