Skip to content
Home » Maganin Biebities: Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga

Maganin Biebities: Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga

Diebities cuta ce wadda take yawan damun mutane wanda a hausance ake ce masa ciwon suga a hausance, wanda yake damun mutane da yawa a fadin duniya, a cikin wanna post din inshallahu zamuyi magana akan wani maganin mai sahihihanci wanda yake taimakawa wajen magance diebities da ikon Allah wanda an jaraba kuma ana samun lafiya.

Maganin Diebities

Minene Diebities (Ciwon Suga)

Diebities cuta ce wadda take kama mutane wadda ta dalilin waniu abu na wanda ake cema pancrease a turance kodai ya samu rauni ta yadda baya iya hada wato cells din sunyi rauni ko kuma ya hada da yawa yadda sugar yayi yawa a cikin jini.

A cikin jini idan jiki ya kasa kama sugar na insulin wanda cikinsa akwai glucose wanda yake bada karfin jiki ko kuma yayi yawa tadda jikin bai iya rike shi shine matsala take samuwa.

Cuta ce wadda ake samunta wani lokacin ta hanayar gado, wani lokacin kuma kama mutum hakanan take musamman mutanen da suka manyanta dukda har ma yaran tana kamawa.

Karanta: Maganin Ciwon Ido: Hanyoyin da Zaka bi Wajen Magance Ciwon Ido

Muna kala-kalar Diebities a wannan zamanin wanda sune kamar haka.

Ire-Irensa

Ciwon suga ya rabu zuwa gidaje ne wanda suka hada da:-

Type 1

Wani irin diebities ne wanda wasu daga cikin cells ko kwayoyin gini na cikin pancrease, suke mutuwa ko su lalace yadda basu iya hada abunda mukayi magana a baya wato insulin.

To idan suga samu matsala hakan yana iya haifar da karancinsa sosai a cikin jini, kuma akwai hanyoyin na fili da wanda suke jan lalacewa ko bacin irin wadannnan abubuwa.

Type 2

Sai kuma akwai fannin na biyu wanda shi a turance ake cema type 2 shi kuma yadda yake shine,  pancres tana haifar da insulin mai yawa a cikin jini wanda jiki babu yadda zai yi da shi.

Hakan yake sa sugar dake cikin jini yayi yawa yadda zai kawo matsala.

Gestational diabetes

Shi kuma wani na’uin diebities ne wanda yake shafar masu ciki, kuma mafi yawanci mutanen da daman a tarihin iyalinsu wato a zuri’aarsu akwai masu diebities.

Shi yadda takd shine yana faruwa ne a dalilin toshewar hormones wanda suke hada insulin a lokacin da mace take dauke da ciki, wanda wannan na’uin kuma yawanci yana kjomawa zuawa na sama da muka yi bayani wato type 2.

Alamominsa

Wannan ciwo wato na suga yana da alamominsa idan mutum yana dauke daa shi kuma gasu kamara haka a lissafe:L-

  • Yawan yin fitsari
  • yawan kaikai a kan fata
  • gani bijibiji
  • Rashin saurin warkewar ciwo idan aka ji ciwo a fata ko kuma a gaba

Karanat: Maganin Ciwon Ciki Cikin Karamin Lokaci

Maganinsa

yadda za’a magance shi a gargajiyance shine za’a samo shuwaka wadda ake yin abinci da ita ko kuma ince miya zaka ga tana da daci sosai.

Daga nan kuma sai a samu tsamiya wannan wadda aka sani ana yin kunu a samu mai kyau kuda ukku haka ko biyu kuma hudu mai kyau.

Sai a wanke shuwaka saboda dacinta wanki na farko zai fara fidda dacin, a kara na biyu a kara har ma na ukku a wanke shuwakar yadda za’a rage mata daci.

Daga na sai a samu kamar rabin kalan na ruwa a sa shuwakar da kuma tsamiyar ta dan yi kamar awa biyu ko ukku haka dai sun jiku sai a rika diba ana sha safe da lokacin dare.

To inshallahu idan yayi yawa zaiyi sauki idan kuma daman mutum na da shi zai samu sauki ya rika ragewa yadda ko abincin zai iuya ci.

Wannan hadin da izinin Allah ana samun saukin diebities saboda an jaraba shi sosai kuma an samu sauki.

A kula dai ana yi ana yin kwaji test yadda za’a fahimta, mungode.

Karanta: Maganin Yawan Kasala a Jiki