You are currently viewing YADDA AKE HADA MAN RIDI (SESAME OIL)

YADDA AKE HADA MAN RIDI (SESAME OIL)

Yadda ake hada man ridi abu ne mai sauki wanda kamar yadda kowa ya sanai yada da amfani a jikin mutum da kuma lafiyarshi kuma shi ridi kamr yadda kowa ya sani abu ne wanda ana samun shi a kasarmu ta Nigeria ana noma shi.

To kafin mu tafi zuwa yadda ake hada shi bari da farko mu fara yin bayani akan amfanin man ridi da yake yi a jikin mutum.

yadda ake man ridi

Amfanin Man Ridi

  • kare jiki daga kamuwa da cuttuttuka
  • Yana taimakawa wajen rage yawan sugar dake jikin mutum
  • Ana shafa ma gabobi domin rage radadi
  • yana taimakawa wajen saurin warkar da ciwo
  • Yana kara karko da kuma kaurin gashi

 

YADDA AKE SISAME OIL (MAN RIDI)

     Dafarko za’a samu ridi a tsince shi a gyara sai akaishi a nukashi wurin masu nika agusi. Zakasamu roba kazuba a ciki sai a yayyafa ruwan dumi sai kasa hannu kana muzawa sosai da sosai kanayi kuma kana yayyafa ruwan dumin haryafa fidda mai kana kwashe har sai man yafita duka sai kasamu container azuba.

Karanta:

Yadda Ake Amfani da WPS Software

Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari