Ciwon ido ciwo ne da mutane da dama suke fama da shi wanda kuma matsaala ce babba wadda idan aka ce mutum ba ido ko ya samu matsalat ido dudda bai mutu ba amma ai yayi mutuwar tsaye.
Shiyasa a cikin wannan post din zamu yi bayani akan wasu magunguna ciwon ido da shi mai lalulurar zai yi amfani da su da kuma hanyoyin da ko shi mai lafiya zai rika bi domin kara karfin idonsa.
Table of Contents
Ya Ciwon Ido Yake?
ciwon ido lalura ce wadda takan shafi duka maza da mata wanda yadda ake saurin gane wanda yake dauke da lalurar shine zaka ga kwantsa ta cika wajen idon kuma idon yayi ja.
Kaikayi da zafi zai damu mai ciwon sai dai ya danganta da yanayin ciwon karami ne koko babba ne wanda zaka ga suuna fama da yanar ido.
To ko da ace lafiyar ka lau ka rika kulawa da idanununka ta yadda kafin cutar ta zo ta riske ka ya kasance ba wai sakaki kayi ba kawai kaddara ce daga wajen Allah.
Karanta: Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam
Maganin Matsalar Ido
Na daga cikin maganin da ake yawan amfani da shi na gargajiya gasu kamar haka ya danganta wanda mutum ya dauka kuma duka suna yi cikin ikon Allah.
Kawallin Itatuwa
Akwai wasu itatuwa guda ukku wanda ake yawan amfani da su musamman ga masu fama da matsalar idanu ko kuma shekaru sun ja.#
Shi wannan wanda zan fadi koda ace lafiya lau kana iya yinsa wanda mutane da yawa na cewa yanayi cikin ikon Allah, Amma kasan magani yayi ma wani yaki yima wani sai dai ko wannan kuma.
Yadda ake shine za’a samu itatuwan da zan lissafa su kuma kowane kwallon shi ne ake samu, gasu kamar haka:
- Dabino
- Hulba
- Habbatus Sauda
Za’a samu kwallon wadannan tsiran da na amfbata sai a kona su suyi baki, su zama gawayyiu daga nan kuma sai a samu abun dakawa a daka su sosai su daku.
Bayan sun daku sai a tankade ana eaba tsakanin tsakin da kuma mai kyan , su daku sosai to sai a samu wani wuri a zuba a samu abun shafawa kamar kwaalli.
Karanta: Hanyoyi 5 Masu Amfani Domin Magance Hawan jini
Kullun mutum ya tsahi da safe ya shafa kuma haka lokacin dare ma ya rika shafawa ya dauki aa rana ta faarko da ka fara yi bayan ka tashi da safe misali idan da daddare ne amfi so ma ka fara shafaw a a lokacin dare.
To zakagaa ya wanko maka kura tsakuwa da kuma duk wasu dattin da suka dade a cikin idonuwan, da ka samu madubi zaka gansu kamar kwantsa saai ka cire.
Bayan karamin lokaci karamar lalurar ido inshallahu za’a samu saukinta in kuma tayi babba sosai sai a tafi wajen likati wannan abun ko mai lafiya ana son ya rika yinsa.
Karanta: Illolin da Ruwan Sanyi yake da Su a Jikin Mutum
Farin Kwalli
Farinkwalliyana da matukar amfani sosai kuma yana kare idanu daga saurin kamuwa da cututtuaka sannan kuma yana kara taimakawa sosai wajen gani a idanu.
Don haka ana so mutum yaa rika amfani da shi in baka iyawa koda sau daya ne a rana domin yana magance cutukan idasnu mai fama da lalurar ido ya rika safashi koda sau biyu ne ga karamar ciwo.
Karanta: Amfanin Yawan Shan Ruwa 6 ga Lafiya da Yakamata a Sani
Hanyoyin Kara Karfin Ido
Ga wasu daga cikin muhimman hanyoyin da suke taimakawa wajen samun karfin idanu tare da kare shi daga saurin ka,muwa da cututtuka idan aka sa kula.
- Kaucewa amfani da farafar papper a cikin rana
- Yawan amfani da san ya sunglass ko photocronic glass wanda yake saita haske.
- Cin abinci mai gina jiki musamman fannin da ya shafi kifi d akuma vitamin A, C da sauransu.
- Kaucewa karatu a cikin karancin haske.
- Kaucewa yawan taba idanu da hannayen da basu da kyau.
Author Profile
Latest entries
- UncategorizedAugust 16, 2024YADDA AKE HADA WEBSITE A KYAUTA DON BUNKASA KASUWANCI
- KasuwanciAugust 16, 2024Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi
- KasuwanciAugust 16, 2024kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa
- KasuwanciAugust 16, 2024Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai