Gyaran Fata: Hanyoyi 5 da ake Gyaran Fata da Fuska da su

Gyaran fata ko fuska da kula da asu abu ne wanda kowa yake kansa musamman ma samari da yan mata saboda suna wadanda suke da kurciya yanzu suke girma, dalilin haka ne a wannan rubutun mukayi i dubi zuwa wasu muhimman hanyoyin da ke gayara fuska ko fata cikin sauki

Hanyoyin Gyaran Fata Da Fuska

gyaran fuska ko fata da maganin pimples

Gayen guava idan ka sameshi ka wanke shi sai ka sai ka sa ruwa a tukunya a tafasa shi sosai sai a dunga sha da ɗumi-ɗumi. Idan kanaso zaka iya zuba sugar ko zuma.

yana taimakawa sosai wajen maganin pimples ko kurajen fuska a jikin mutum.

Gyaran fata da Dankalin Turawa (Arish potattas)

          Dafarko zaka wake arish ɗinka sai kayi blending ɗinshi bayan ka fere sannan sai kayi stiming ɗin fuakarka da ruwan ɗumi sai ka shafa a fuska kabarshi yayi kamar 30minutes sai ka wanke.

Gyaran Fata da Cocumber

          Farko zaka samu cocumber ɗinka ka wanke sai kayi blending ɗinta,zakayi stiming  fuskarka sai ka shafa cocumber ɗinka yayi kamar 20minutes sai a wamke.

Ganyen Magarya

Kamar yadda muka ambata a post dinmu Ganyen magarya yana magugun guna da yawqa kamar yadda a baya mukayi magana da bayanin akan yadda ganyen magaraya yake gyara jikin mutum, to a kuraje ma yana taka rawa sosai.

za’a samu dakakken ganyen magarya sai a samu wuri a kwaba da ruwa  yayi kumfa daga nan kuma sai a rika shafa ma fuska  a shafe ta duka a bar shi yayi karanci minti talatin.

Amfanin shine yana maganin kuraje kuma yana sa jiki tafshi tare wanke dauda a saman fatar mutum.

Karanta:

Lemun Tsami

Abu na gaba kuma shine lemun tsami wanda a kimiyyance lemun tsami yana wanke dauda da cututtuka a jikin dan adam, to a fannin fuska ma idan kuraje suka dame mutum ana yanka shi sai a rika shafawa a fuska inshallahu cikin karamin lokacin za’a samu saukin su.

Karanta:

 

 

 

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari