Gyaran gashi, lafiyarshi, abunda ya shafi kyan fata da lafiyarta abu ne mai matukar amfani musamman ga mata asaboda mace dole sai da tsafta, a wannan post din zamu kawo maku cikakken bayani wanda wata hukuma a America tayi akan yadda wasu muhimman abincicika dake kara lafiyar wadannan gabobin.
Yana da kyau a fahimci cewar , fata ko kuma akaifa bawai kawai kayan shafe shafe ne ke taka rawa ba a’a abincin ma da ake ci shima yana taka rawa sosai wajen sanya kyawan gabobi da kuma kara masu lafiya sosai.
Table of Contents
Ta yaya abinci ke Gyara Gashi, Fata ko Akaifa
A wani binciken da kungiyar da ke kula da kiwon lafiyar cimaka da jikin mutum ta Amerika tayo a 2020 wato National Library of Medicine a kan abinci ta gano cewa,
Yanayin abinci wanda yake kunshe da kayan marmari da kuma kayan lambu yana habbaka lafiyar gashi sosai da kuma kara mashi kyau.
A binciken sun gano cewa cin abubuwan ko kayan ganye yana taimakawa wajen gyara gashi sosai, su kuma wandanda suka shafi kayan lambu haka suna taimakawa wajen akaraa lafiyar fata da kyanta.
Sai kuma a dayan bangaren kuma cin abubuwa masu mai da kitse akwai musamman irin kifi yana da wni sinadari da ake kira da omega-3 acid yana taimakwa wajen habbaka lafiyar gashi da kuma fata.
To kamar yadda binciken ya wakana a takaice dai wadannan nauin abincin suna taimakawa sosai wajen habbaka lafiya r wadannan gabban da muke magan akansu wanda gasu kamar haka zamum lissafa.
Nauin Abincin da Ke Taimakawar a Lissafe
- Kifi
- Kwai
- Avokado
- Kankana
- Kabeji da lattace
- Dankali
- Apple
- Gyada
- Albasa
- Tumatir
Wadannan abincin da muka ambata suna taimakawa sosai kamar yadda binciken ya gabata sai kuma akwai wadanda suke kawo akasi ga lafiyar wadannan gabban kamar haka
Karanta:
Abincin da Ke Kawo Nakasa Garesu
Yawancin Abincin da akayi processing daga company aka sa mashi chemicals, gas ko kuma suga suna yawan lahanta wadannan gabobin.
Shiyasa duk abunda zaa saya masu kiwon lafiya suke bada shawarar a sayi wanda ke fresh ban kamfani ba yafi kyau saboda ana kara masu preservetives masu sa abu kar yayi saurin rubewa da kuma chemicals wanda jiki baya son su.
Karanta:
Author Profile
Latest entries
- UncategorizedAugust 16, 2024YADDA AKE HADA WEBSITE A KYAUTA DON BUNKASA KASUWANCI
- KasuwanciAugust 16, 2024Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi
- KasuwanciAugust 16, 2024kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa
- KasuwanciAugust 16, 2024Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai
delta 8 near by