Skip to content
Home ┬╗ Amfanin man kadanya ga fatar Dan Adam

Amfanin man kadanya ga fatar Dan Adam

Asalin man kadanya wata shukace dake fitowa ta girma har takai gayin ‘yaya, wadanna ‘yayan ana shansu domin suna da dadi sosai sannan kuma ana anfani dasu ta hanya daban-daban wurin magungunna.

Misali: ga fatar Dan Adam, gyaran gashi, Faso da sauransu.

Wannan shuka ta kadanya takan fito wurare da dama musamman ma a gonakai.

Toh yanzu zamuji kadan daga cikin anfanonin da man kadanya keyi.

Anfanonin

1) laushin fata

2) kawar da zanen haihuwa

3) man lebe

4) kawar da kuraje

5) hana karyewar gashi

  • Laushin fata

Yana taimakawa fatar jiki musanman ma wadan da suke fama da gautsin fata, za’a rika shafashi duk lokacin da akayi wanka domin yazamana shine man shafawa.

  • Kawar da zanen haihuwa

Yana kawar da zanen haihuwa Wanda ake kira a turance da (stretch marks), wanda yake fitowa mata masu juna biyu, to a lokacinda mace mai juna biyu taga sunfito mata abunda zatayi shine; sai tasamu man kadanya tarika shafawa aka zanen har sai taga sun bace.

  • Man lebe

Ana anfani dashi wanjen man lebe, domin Yana hana fashewa da kuma bushewar lebe, sannan kuma Yana sa laushi dakuma kyawun lebe.

  • Kawar da kuraje

Idan kuraje suka dame ka/ki to tabbas ki/ka rika shafa masu man kadanya akai akai idanma da sone ki/ka maidashi man shafawa na yau da kullum.

  • Hana karyewar gashi

Man kadanya na taimakawa sosai wajen gyaran gashi, domin Yana sa gashin kai ya karu, kuma hakan na rage karyewar gashin dakuma sanya gashin sheki.

Domin gashi Yana bukatar arika samashi mai me danko bayan an wankeshi.