Skip to content
Home » Magungunan da habbatussauda keyi a jikin dan adam

Magungunan da habbatussauda keyi a jikin dan adam

Habba na daya daga cikin mafi anfanin kwaya  dake taka rawa wurin kiwon lafiyar dan adam, duba da irin sinadaran da take dauke  dasu.

Habba na daya daga cikin magungunan musulunci Wayanda ake anfani dasu ta hanyoyi da dama, wannan kwaya ta habba bawani girma garetaba sannan kuma bakakene wadan da akan sarrafasu sufitar da mai.

magungunan musulunci na habbatus sauda

Yanzu zamuji kadan daga cikin magungunan da habba keyi.

Magungunan da Habbatus Sauda Ke Yi

1) maganin ciwon kunne

2) maganin kunburin jiki

3) maganin kunburin muka-mukai

4) maganin sanyi

5) maganin ciwon zuciya

6) maganin kunburin Anta

7) maganin ciwon makogwaro, Mara, ciki da basir.

8) maganin rashin bacci

9) maganin sauro da aljanu

10) maganin olsa

11) gyaran jiki

12) rage tumbi

Yadda zaku hada

1. Maganin ciwon kunne

Idan ana ciwon kunne anaso asamu man habbatussauda ba yayantaba da man albasa a hadesu wuri guda. Arinka shafawa koda yaushe duk lokacin da akasa sai a samu auduga a toshe kunnen saboda gudun likewar kura.

2. Maganin kunburin jiki

Da kwai ciwo da dama dakansa jikin dan adam yayi kunburi alokacin da yake yinsu ko kafin yayi kokuma ma  bayan ya gama, to idan hakan ta faru abunda za’ayi shine a samu man habba arinka shafawa kuma ana sha.

3. Maganin kunburin muka-mukai

Idan mummuke yayi kunburi to a samu man habba da albasa asha kuma sana arinka shafawa awurin har sai ya sabe.

4. Maganin sanyi

Habba na taka rawa sosai wajen yin maganin sanyi, yadda za’a hada shine a samu mono ahadashi  da man habba ko garinta a cakudesu a rika shafawa.

5. Maganin ciwon zuciya

Za’a tafasa ruwan zafi  kokuma a Samu shayin da beda lifton acikinsa wanda aka dafashi da na’a na’a kokuma green tea, sai a samu habba karamin cokali da Zuma asa cikin ruwan zafin a riaka sha koda yaushe.

6. Maganin kunburin hanta

Za’a tafasa ruwa sannan a samu garin habba Dana kurna kowane teaspoon daya atafasa da ruwa arinka sha.

7. Maganin ciwon makogwaro, Mara, ciki da kuma basir

Za’a samu

* habbah  teaspoon 10

* suga teaspoon 6

Yadda za’ai shine a samu garin habba da suga ahadesu arika sha kafin aci komai da kuma bayan anci da awa daya.

8. Maganin rashin bacci

Abubuwan da ake bukata sune:

  • Habba teaspoon daya
  • Zuma teaspoon ukku
  • Madarar ruwa gwan-gwani daya

Yadda ake hadawa shine  za’a samu madara a kara mata ruwa kadan sai a samu habba cokali daya sai Zuma cokali ukku sai a daura akan wuta Jim kadan a sauke.

Sai mai matsalan yayi alwala sannan yasamu wannan hadin yakaranta masu wadannan ayoyin na ayatushshifa sannan ya sha.

9. Maganin sauro da aljanu

Asamu garin habba arikayin hayaki dashi a gida domin yana magance abubuwa da dama musanman ma kwari masu cutarwa kamar irinsu; tsaka, kunama, maciji sauro da sauransu kai harma mutumin da Ke dakwai cuta acikin ranshi.

Ammfa anfiso a samu tsaban habba, domin yana magance zaman aljanu masu cutarwa su tafi gabadaya.

10. Maganin olsa

Za’a samu;

  • Habba teaspoon shida
  • Hulba teaspoon shida
  • Zuma Kofi daya

Za’a samu duka wadannan a hadesu waje daya, sai wanda yake fama da cutar yarika sha awa daya kamin yayi kalaci da rana ma haka sai kuma da daddare awa daya bayan cin abinci.

Karanta:

 Magunguna 5 da ya Kamata su Kasance Tare da Kai a Kullun

Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam

11. Gyaran jiki

Za’a samu man habba da na zaitun a hadesu wuri guda arika shafa ma jiki domin yana Sa jiki yayi kyau kuma yana bada kariya daga shedanu.

12. Rage tumbi

Za’a samu man habba, man albasa, man jirjir da kuma zaitu lauz ahade su wuri daya azuba Zuma aciki arika sha yana rage tumbi sosai.

Karanta:

Abinci guda 10 Wanda Suke Sa Lafiyar Gashi, Fata da Akaifa

Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam