Habba na daya daga cikin mafi anfanin kwaya dake taka rawa wurin kiwon lafiyar dan adam, duba da irin sinadaran da take dauke dasu.
Habba na daya daga cikin magungunan musulunci Wayanda ake anfani dasu ta hanyoyi da dama, wannan kwaya ta habba bawani girma garetaba sannan kuma bakakene wadan da akan sarrafasu sufitar da mai.
Yanzu zamuji kadan daga cikin magungunan da habba keyi.
Table of Contents
Magungunan da Habbatus Sauda Ke Yi
1) maganin ciwon kunne
2) maganin kunburin jiki
3) maganin kunburin muka-mukai
5) maganin ciwon zuciya
6) maganin kunburin Anta
7) maganin ciwon makogwaro, Mara, ciki da basir.
8) maganin rashin bacci
9) maganin sauro da aljanu
10) maganin olsa
11) gyaran jiki
12) rage tumbi
Yadda zaku hada
1. Maganin ciwon kunne
Idan ana ciwon kunne anaso asamu man habbatussauda ba yayantaba da man albasa a hadesu wuri guda. Arinka shafawa koda yaushe duk lokacin da akasa sai a samu auduga a toshe kunnen saboda gudun likewar kura.
2. Maganin kunburin jiki
Da kwai ciwo da dama dakansa jikin dan adam yayi kunburi alokacin da yake yinsu ko kafin yayi kokuma ma bayan ya gama, to idan hakan ta faru abunda za’ayi shine a samu man habba arinka shafawa kuma ana sha.
3. Maganin kunburin muka-mukai
Idan mummuke yayi kunburi to a samu man habba da albasa asha kuma sana arinka shafawa awurin har sai ya sabe.
4. Maganin sanyi
Habba na taka rawa sosai wajen yin maganin sanyi, yadda za’a hada shine a samu mono ahadashi da man habba ko garinta a cakudesu a rika shafawa.
5. Maganin ciwon zuciya
Za’a tafasa ruwan zafi kokuma a Samu shayin da beda lifton acikinsa wanda aka dafashi da na’a na’a kokuma green tea, sai a samu habba karamin cokali da Zuma asa cikin ruwan zafin a riaka sha koda yaushe.
6. Maganin kunburin hanta
Za’a tafasa ruwa sannan a samu garin habba Dana kurna kowane teaspoon daya atafasa da ruwa arinka sha.
7. Maganin ciwon makogwaro, Mara, ciki da kuma basir
Za’a samu
* habbah teaspoon 10
* suga teaspoon 6
Yadda za’ai shine a samu garin habba da suga ahadesu arika sha kafin aci komai da kuma bayan anci da awa daya.
8. Maganin rashin bacci
Abubuwan da ake bukata sune:
- Habba teaspoon daya
- Zuma teaspoon ukku
- Madarar ruwa gwan-gwani daya
Yadda ake hadawa shine za’a samu madara a kara mata ruwa kadan sai a samu habba cokali daya sai Zuma cokali ukku sai a daura akan wuta Jim kadan a sauke.
Sai mai matsalan yayi alwala sannan yasamu wannan hadin yakaranta masu wadannan ayoyin na ayatushshifa sannan ya sha.
9. Maganin sauro da aljanu
Asamu garin habba arikayin hayaki dashi a gida domin yana magance abubuwa da dama musanman ma kwari masu cutarwa kamar irinsu; tsaka, kunama, maciji sauro da sauransu kai harma mutumin da Ke dakwai cuta acikin ranshi.
Ammfa anfiso a samu tsaban habba, domin yana magance zaman aljanu masu cutarwa su tafi gabadaya.
10. Maganin olsa
Za’a samu;
- Habba teaspoon shida
- Hulba teaspoon shida
- Zuma Kofi daya
Za’a samu duka wadannan a hadesu waje daya, sai wanda yake fama da cutar yarika sha awa daya kamin yayi kalaci da rana ma haka sai kuma da daddare awa daya bayan cin abinci.
Karanta:
11. Gyaran jiki
Za’a samu man habba da na zaitun a hadesu wuri guda arika shafa ma jiki domin yana Sa jiki yayi kyau kuma yana bada kariya daga shedanu.
12. Rage tumbi
Za’a samu man habba, man albasa, man jirjir da kuma zaitu lauz ahade su wuri daya azuba Zuma aciki arika sha yana rage tumbi sosai.
Karanta:
Author Profile
Latest entries
- UncategorizedAugust 16, 2024YADDA AKE HADA WEBSITE A KYAUTA DON BUNKASA KASUWANCI
- KasuwanciAugust 16, 2024Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi
- KasuwanciAugust 16, 2024kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa
- KasuwanciAugust 16, 2024Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai