Skip to content
Home » Yadda ake hada kazar amarya

Yadda ake hada kazar amarya

Uhumm! hausawa dai sunce a gidan amarya komai Sabone amma banda Abu 1 toh shiko wannan Abu dayan ko menene?.

To kardai kushagala mutafi kai tsaye tare daku domin sanin yadda ake wannan kaza.

Kayan hadin da ake bukata wajen yin wannan kaza sune:

Kayan hadin

  • Kaza
  • Kayan miya
  • Nonon rakumi
  • Garin ridi
  • Maggi/gishiri
  • Citta
  • Mai
  • Zuma
  • Ruwa

Yadda ake hadawa

Asamu kaza budurwar kaza wadda bata fara kwai ba, a yankata a kwashe duk kayan dake cikinta.

Sannan adan dafata acikin ruwa, amma kar ta ida dahuwa sai a cire.

Sannan ki soya kayan miyarki tare da mai dakuma citta, idan yasoyu sai ki zuba maggi/gishiri dakuma ruwa kadan aciki, wato kitsaida ruwa.

Sai ki zuba nonon rakumin, garin ridi dakuma zummuwa aciki kirufeta tadahu.

Toh idan tadahu anaso kicinyeta kekadai batare da kin rage wani abuba.

Bayan kin gama dahuwar kazarki anaso kisamu; garin ridi ki hadashi da madara kokuma madarar rakumi kimotse kirika sha.