Skip to content
Home » Yadda ake simple make up (kwalliya)

Yadda ake simple make up (kwalliya)

Tabbas yar’uwa ko kinada kyau to ki kara da kwalliya domin ita kwalliya wata adoce da akasan mata dashi.

Tun daga yara mata, yan mata, matan aure Ke harma da dattijai.

Toh ayau inasan in wayar mamu da kanmu akan yadda zamu kware abangaren kwalliya.

Yar’uwa ayanxu zan lissafo wasu daga cikin kayan kwalliyar mu da muke dasu, kuma wadanda zamuyi amfani dasu.

Kayan kwalliya

  • Foundation
  • Janbaki
  • Concealer
  • Lip gloss (man baki)
  • Maskara
  • Kwalli
  • Eyeliner
  • Eye Shadow
  • Eye pencil da sauransu.

Acikin wannan kwalliya zamubi matakai guda bakwai kadai sune.

Matakan

1) wanke fuska

2) abun shafa foundation

3) yadda zaki shafa foundation

4) amfani da eye pencil

5) shape din baki

6) rage girman baki

7) taje gira

Yadda akeyi

1) wanke fuska

Zaki fara wanke fuska wato ki tsaftaceta, saboda gudun samun kuraje da cututtukan fuska.

2) abun shafa foundation

Ki samu foundation kalar fuskarki, kidauko abun shafa foundation dinki kijikashi da ruwa sai ki matse.

To dashi zakiyi amfani wajen shafa foundation dinki.

3) yadda zaki shafa foundation

Dafarko zaki iya sashi a bayan hannu kina dangwalowa kina shafawa, zakuma ki iya diddigashi a fuskarki.

Sai kidauko form din shafa foundation ko powder bayan kin jikashi Sai kimatse.

Kifara bin fuskarki kina shafe foundation din, ammafa ki dingayi a hankali kina daddannawa har Sai kinga yabi fuskar ya kwanta luf.

4) amfani da eye pencil

Sai kidawo kan bakinki ki shafa man baki kadan saboda yasa bakin taushi, zakuma ki iya amfani da Basilin tunda ba’aso man yafito.

Daganan sai kiyi lining da eye pencil, in kuma kina amfani da bakar eye pencil to Janbakinki ki tabbata mai haskene.

Amma in bazakiyi amfani da eye pencil ba to zaki iya amfani da kowane irin janbaki.

5) shape din baki

In kin shafa man baki ko basilin sai kiyi lining amma ki tabbata kinfitar da shape din bakinki da kyau musamman ma lebenki na sama.

Ki tabbata kin fitar da wannan “V” shape din saboda shi ke karama labbanki kyau da kuma kara fito da kwalliyar baki daya.

Kiyi layin eye pencil din lafiya lau Kar wani wuri yafi wani cizawa.

Sai ki shafa janbaki mai Dan haske a tsakiyan amma in kina amfani da burawun eye pencil to zaki iyasa Jan janbaki, sai kisa man baki sannan kisamu concealer koh eye Shadow mai haske; kamar golden ko fari dasauransu ki shafa a tsakiya.

6) rage girman baki

Sai kizo kiyi concealing din bakinki saboda shape din yafito sosai kuma yarage girman bakin.

To daganan zaki iya shafa powder sai kisa eyeliner basai kinsa eye Shadow ba kisa maskara kisa kwalli saboda yakara fitowa da shape din idonki.

7) taje gira

Kiyi amfani da abun maskara ki taje gashin girarki ammafa ki tabbatar kin share maskaran dake jiki ya rage kadan saboda ya karama giranki baki da kyau.

Kuma sai ki kara bin fuskarki da powder ki gyarata, takwanta sosai.