Skip to content
Home » Amfanin Yawan Shan Ruwa 6 ga Lafiya da Yakamata a Sani

Amfanin Yawan Shan Ruwa 6 ga Lafiya da Yakamata a Sani

yawan shan ruwa yana da matukar amfani ga lafiyar mutum kuma duk wanda a rana yake yawaita shan sa yana taimakamasa sosai ta fuskar inganta lafiyarasa, shiyasa a yau a cikin wannan post din zamu yi bayani akan wasu amfanunnukan da yake yi a cikin jin mutum.

Wasu mutane da dama zaka ga idan suka shagala da wani abu sai kaga sun bar shan ruwa, wanda basu san cewa hakan matsala ce sosai da kuma barazana a lafiyar jikinsu musamman ma bayan cin abinci ana son mutum ya sha ruwa da yawa ta yadda abincin nasa zai samu juyawa sosai.

yawan shan ruwa

Saboda mi Ake son yawan shan Ruwa

A cikin jikin kowa ne mutum da Allah ya halitta kusan kashi sittin dinsa ruwa ne sauran kason ne wasu abubuwan kan iya biyo wa a baya.

Kuma kamar yadda binciken masana ya bada shawara ana son kowane mutum a duk rana ya zama ya sha lita 237 na ruwa shine jikinsa zai samu yadda yake so.

karanta: Maganin Yawan Kasala a Jiki

karancinsa yana saurin haifar da cuttuka kuma yakan sa rauni wajen magance cutukan da suka kiusan warkewa wanda hakan illa ne a jiki da kuma garkuwar jikin.

Samun Kuzari

Ga mai son yawan samun kuzari da kuma karfi a cikin jikinsa ya yawaita shan ruwa musamman ma ruwan da basu da sanyi, domin yawan shan ruwan sanyi yana da illa sosai a cikin jiki kamar yadda muakyi bayanin illolin  yawan shan ruwan sanyi a baya.

Amma shan ruwan zafi bai cika kawo illa a jikin mutum ba kamar dai na sanyin saboda shi na sanyi yana saurin dasjkae cutuka wanda shi kau na zafin kokarin kashe su yake.

Saurin Narkar da Abinci

bayan ka ci abinci ana son ka sha isasshen ruwa wanda zai bada damar juya abincin yadda ya kamata saboda da ruwa abincin yafi saurin narkewa ga uwar hanaji.

ka kula kuma ba’a maye wasu abubuwa da sha a ce wai maimakon a sha rjuwa misali kayi ta shan lemu kace ai yau ba sai ka sha ruwa ba wannan illa ce.

saboda jikinka yana bukatar taceccen ruwan shikau lemun da zaka sha na kamafani anyi ittifakin kan cewa yana da illoli da dama a lafiyar mutum musamman chemicals dinda ake samasa don kar ya lalace wand ake kira preservatives.

karanta: Hanyoyi 10 Domin Karin Kiba a Jikin Mutum

Magance Tsakuwar Kwada

Ga masu fama da cutar tsakuwar kwada yawan shan ruwa yana yana taimakawa wajen magance ta sosai kamar yadda rashin yawan saha yana saurin haifar da ita.

mai fama da irin wannan larura ana son ya yawaita shan ruwa ta yadda ruawan zai narkar da duwatsun ada ke cikin kwadan wato abubuwqan da suka cure na sinadarai.

Rage Yawan Nauyin Jiki

Yawan sahan ruwa yana taimakawa sosai wajen rage nauyin jiki wanda yake taimakawa wajen rage kiba a jikin mutum, saboda yawan nauyi a jikin mutum kamar yadda mukayi bayani yana saurin haifar da hawan jini, diebities da sauran cutukan da ake yawan fama da su a wannan zamani.

Samun Saukin Sikila

Yawan shan ruwa yana taimakwa masu fama da larurar ciwon sikila wanda damar curwar red blood cells ke tada abun, to cikin ikon Allah idan mai fama da lalurara yana yawan shansa yana sa magudanar jini ta gudana sosai.

Kuma hakan ne iska zai samu damar zagayawa a cikin jikin ta yadda zai kwantar ko ya rage radadin a lokacin da abun ya taso, in kuma bai taso ba ya taimaka wajen kariya.

Karanta: Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam