Skip to content
Home » Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

Kamar yadda a baya muka yi bayani akan hanyoyin da ke taimakawa wajen kara kiba cikin sauri to a yau kuma inshallahu zamu yi magana ne akan wadanda ke taimakawa wajen rage yawan kibar jiki da ta tumbi.

Hanyoyin Rage Kiba.

Kiba ga wasu halitta ce wanda daman cen Allah yayi su masu kiba ko suna ci komin yadda sukayi sai dai ta dan ragu, to amma akwai wanda daga baya suke samun kibar su wadda wani lokacin ma kusan har ma yawa ta ke yi masu.

Kibar da tayi yawa wato wadda ba ta halitta ba masu ita wani lokacin ma har kasa tashi suke saboda yawan nauyin jiki ga kuma tumbi, amma yawanci lafiyayayyar ita zakag basu jin sun kasa tashi.

Yawancin abunda ke haifar da kiba kitse ne wanda in yayi yawa yake tshe hanyoyin jini ta yadda baza su samu sukunin zagayawa ba.

Rage KIbar Juki ko tumbi

Sanadiyyar hakan yana saurin haifar da ciyuka na zamani wanda suke yawan addabar mutane kamar su:-

  • Hawan Jini
  • Ciwon Sugar
  • Ciwon Gawut da sauransu

mafi yawancin binciken da masani kiwon lafiya suke yi sun tabbatar da wasu hanyoyi da mutum zai bi domin rage kibar jiki da ta tumbi wanda ga su kamar haka:-

Rage cin Kitse

Yawaita cin kitse yana daya daga cikin babban abunda ke haifar da kiba a cikin jikin mutum saboda shi kitse yana dauke da sinarin cholesterol wanda kusan bayan markade aabincin yana tsayawa a matsayin sa na kitse a kaso mai yawa.

Bayan haka kuma ba’a so yana yawa a cikin jini saboda gudun kar ya rika toshe hanyoyin jini da ke kaima zuciya, wanda hakan ma kuma yana taimakawa wajen haifar da hawan jini.

Karanta:

Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam

Yawan Motsa Jiki

Motsa jiki nada mahimmaci ga kowane mutum, kuma yinsa ko yaya ne yafi rashin yinsa gabakidaya.

Abunda masana suka ce kusan ana son kowane mtum a rana kar ya gaza motsa jikinsa na akalla da minti 30, yin hakan yana taimakawa wajen inganta lafiyars da kuma kare shi daga cututtuka masu barazana ga rayuwar Dan Adam.

Yadda motsa jiki ke taimakawa wajen rage kiba shine yana taimakwa wajen kona ko narkar da calories da sukayi yawa a cikin jiki.

Yawan Yin azumi

Azumi yan taka rawa sosai wajen daidata kiba a jikin mutum, kuma yana taimakwa sosai wajen habbaka lafiyar jiki.

Saboda mutum Sugar na cikin jini yana yin kasa da ta yadda idan yayi yawa zai ragu har ya kai yadda lokacin da za’ayi buda baka a maida wanda aka rasa.

Karanta:

Maganin Ulcer: Yadda zaka magance gyanbon ciki ulcer Babba da karama

Rage Yawan ci barkatai

Yawancin miutanen da suke kiba haka barkatai zaka ga suna da mugun yawan cin abinci ba tsari koda yaushe suka samu kawai sudai su ci.

To hakan yana da illa a lafiya kuma zai sa yawan calories yayi yawa a cikin jiki wanda hakan zai rinka haifar da kitse a cikin jiki har kiba ta taru

Rage Yawan cin Zaki

Yawaita cin abubuwa masu zaki suna saurin sanya kiba musamman kibar tumbi, do haka idana kana bukatar ka rage kibar tumbi sai ka rage yawan cin abu mai zaki.

Karanta:

Hanyoyi 10 Domin Karin Kiba a Jikin Mutum

Rage Saurin Kwanciya bayan Cin Abincin dare

Saurin kwanciya ko kuma ince makara wajen cin abincin dare kuma bayan an ci shi ayi saurin kwancinya yana saurin haifar da kiba.

Bayan nan ma buga da kari illa ce sosai ga lafiya musamman mutum bai gane hakan sai ya tsufa saboda abincin bai narke ba aka fara markade shi mutum ya kwanta hakan yana saurin sanyi abincin ya zama ,mai yawan cholestoral wanda hakan illa ce.