Skip to content
Home » Ruwan Dumi: Amfanin Ruwa Dumi 5 ga Lafiyar Jiki

Ruwan Dumi: Amfanin Ruwa Dumi 5 ga Lafiyar Jiki

Ruwan mai dumi ko zafi yana amfani sosai ga lafiyar jiki kamar yadda a baya mukayi bayani akan illolin da ruwan sanyi yake da su, a fannin ruwa mai zafi abun ba haka yake ba saboda yana da matukar amfani musamman ma lokacin sanyi.

A cikin wannan post din inshallahu zamu yi bayani akan wasu muhimman rawar da yake takawa a lafiyar jikin mutum idan yana sha kuma yana amfani da shi duk da shima a wani fannin yana tashi matsalar.

amfanin ruwan zafi a jikin ga lafiya

Yana Taimakawa saurin Markade Abinci

Ruwan da ke da zafi ko duma shansa yana taimakawa sosai wajen saurin markade abincin da mutum ya ci, idan aya shiga ciki ya kai ga hanji saboda yanayin ciki yanason son zafi.

Musamma a lokacin sanyi wani lokacin yanayin zafin ko yanayin sanyin jiki yakan karu wanda ake bukatar zafi, shan abu mai zafi yana taimakawa uwar hanji wajen saurin markade abincin da aka ci.

Karanta: Ruwan Sanyi: Illolin da Ruwan Sanyi yake da Su a Jikin Mutum

Rage Radadin Sanyi

A lokuttan sanyi yana da matukar kyau murum ya rika yawaita shan ruwan zafi ko ruwan dumi musamman ma da safe ta hanyar haka ne jikinsa zai samu sawaba yadda gabobinsa zasu ji dadin aiki.

Kuma ta hanyar haka ne zai kare jikinsa daga mutuwar jiki yanayin da ke sa mutum yaji gabobinsa duk sun mutu ga kasala baya iya tabuka wani abu ko yayi aiki sosai.

Kuma baya ga sha ana son mutum ya rika wanka da ruwan dumi a lokacin da ake na sanyi ba jarumta bace mutum ya yi wanka da ruwan sanyi a lokacin sanyi musamman da safe yana jawo ma kansa cuta ne musamman ma sai ya tsufa zai fahimci hadarin hakan.

Karanta: Maganin Yawan Kasala a Jiki

Yana Taimakawa wajen Magance Infection

Musamman mata masu yawan fama da matsalar infection a gaba ruwan sanyi yana taimakwa, ana son mace idan zatayi tsarki ta rika amfani da ruwan dumi bana sanyi ba.

Saboda ruwan sanyi yana kara dankarar da kwayoyin cuta da bacteria da suke a wajen baya kashesu ko ya rage su amma cikin ikon alla ruwan zafi duk wata yar karamar kwayar cuta tana mutuwa idan ana amfani da ruwan zafi musamman ma a lokacin tsarki da kuma wanka.

Domin ba karamin alamari bane matsala ce mace ta rika yawan amfani da ruwan sanyi musamman ma a lokacin da ake na yanayin sanyi wanda ruwan ya dauki sanyi sosai.

Karanta:

Amfanin Yawan Shan Ruwa 6 ga Lafiya da Yakamata a Sani

 Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara

Magance Cututtukan Makokwaro

Idan kana son makwokwaronka ya kasance ya zauna lazfiya cikin ikon Allah to ka rike ruwan zafi ka kaucema yawan shan ruwan sanyi,  yadda zan baka karamin misali shine idan ka sha ruwan sanyi yanzu mi zakaji?

Idan aka fahimta a take zakaji kana kakaro majina kuma kasala zata lullubeka, ti haka wuwan sanyi  yake amma ruwan zafi da wuya ka shashi kaji kasala.

Shan ruwan zafi yana kashe bacteria wadda take a makokwaro kuma yana taimakawa wajen magance mura da tari musamman idan aka hada shi a shayi da kayan sanyi kamar su citta da karamfani.

karin Ruwan Jiki

yawan shan ruwa ma ba kawai ruwan sanyi ba yana taimakawa wajen karin ruwan jiki saboda kullun ana son mutum ya sha ruwa kamar lita 8 a jikinsa yadda jikin zai daidaita.

To shi ruwan zafi saboda yana saurin bin jiki ya shiga cikin ciki ana son mutum ya rika yawaita shansa saboda karin ruwan jiki wanda zai taimaka ma jikin wajen gudanar da harkokinsa.

Karanta:

Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga

Maganin Ciwon Sickler da Kuma Bayani akan Cutar

 

 

 

 

Tags: