Skip to content
Home » YADDA AKE KUNUN AYA MAI KWA-KWA

YADDA AKE KUNUN AYA MAI KWA-KWA

Kunun aya wani abun Shane mai dadin gaske wanda hausawa keyi , musanman ma idan yaji kayan hadi dayawa kuma yayi kauri sosai.

Ayau zamu ga kayan hadin da ake anfani dasu wurin yin kunun aya dama yanda ake yinshi.

Kayan hadin:

  • Aya
  • Kwa-kwa
  • Dabino
  • Kanunfari
  • Suga
  • Fulebon kwa-kwa
  • Citta
  • Mataci

Abunda zaki fara da farko shine zaki  dan jika ayarki kadan kamar awa 1, sai ki  barzata a turmi idan kika gama saiki rege ki wanketa ta fita tas ki aje a gefe, sannan ki dauko  kwa-kwarki  ki gyarata sai ki dauko dabino da citta ki wankesu, sai ki dauko ayarki dakika gyara agefe kizuba wadannan dabino, kwa-kwa, citta da kaninfari kizuba aciki sannan ki markada.

Bayan ya markadu sai ki juye shi acikin wuri mai wal-wala kidan kara ruwa kadan ki dama saboda taurinshi, ammafa kada ruwan yayi yawa domin anfison kunun aya da kauri, sai kisa mataci ki tace ruwan sai ki zuba fulebonki mai kamshin kwa-kwa aciki ki motsa sannan kisa a firic yayi sanyi.