Skip to content
Home » Dubulan: YADDA AKE DUBULAN

Dubulan: YADDA AKE DUBULAN

Dubulan de na daya daga cikin abincin da mutane ke ci wanda yake fannin snacks kamar cincin da alkaki an cinsu ne wani lokacin domin marmari ba don yunwa ba kuma, mafi akasari anfi hada bubulan a halin biki ko uma wani shagali da ake yi shiyasa yana da kyau a san ya ake dubulan saboda wata rana.

A cikin wannan post din zamuyi bayani akan yadda ake hada budulan mai kyau da kuma wanda zai amfani lafiyar jikin mutum shi tare da lissafa kayan da ake bukata wajen hada shi wanda gasu kamar haa.

yadda ake budlan

Kayan Hada Dubulan

  • Fulawa
  • mai
  • bekin foda
  • kwai
  • ruwa
  • reza
  • suga
  • lemun tsami
  • ridi/nome

Yadda ake Hadawa

Dafarko idan zaki hada dubulan kika samu fulawarki saiki tankadeta sannan ki zuba bekin foda dadan yawa kamar yadda zaya tashi saiki motsa sannan ki zuba suga da kwai sai kuma ruwa kadan ba dayawaba sannan sai ki kwaba harsai yahade baki daya.

Bayan kin gama kwabinki sai ki samu injin taliya wato wanda akeyin lami dashi saiki runka gutsurar wannan kwabin dubilan din da kadan kadan dede yadda kikeson girmanshi saiki rika sawa wurin yin lamin kinayi amma kada yayi gwabi, idan kuma babu injin taliya ana iya yi da walba ko uma wani luliyayyen katako.

Bayan kingama lamin gaba daya sai ki samu reza kirika dauko wannan lamin naki da dai-daya kina yimashi shape (idan kika dauko daya sai kiyi mashi tsaga hudu a tsakiyar shi sannan kiyi biyu kanana a sama da kasa) yadda zaiyi dadin hadewa yayi kyau.

Karanta: Yadda aKe hada Alkaki a saukake

baccin duk kin kammala saiki zuba manki isashshe acikin kasko idan yayi zafi sai ki ruka daukar wannan dubilan din naki kina zubawa kinadan juyawa da ahankali dan karya darwatse kuma kada kisakar mashi wuta dayawa dan kada yakone idan kika gama soyawa duka saiki tsameshi yatsane.

Daga nan kuma  kisamu sukarinki kizuba cikin tukunya da ruwa madedeci dakuma lemun tsami dede gwargwado ba yadda zai fito ba sai ki daura a wuta ki barshi yayita dahuwa to idan kikaga yana dan danko-danko sai ki sauke shi alamar yadahu kenan.

Karanta: Yadda Ake Hada Cin-Cin mai Gurus Gurus

saiki dauko dubilan dinki dakika soya kirika zubawa cikin ruwan sikarinkina tsamewa kina sawa awuri ,baccin kin kammala duka saiki samu ridinki ko ince nome ki watsa aciki idan kina bukata idan kuma baki bukata sai ki barshi hakanan.

Karanta: 

Yadda ake soya Fara

Waya Hannu: Muhimman Abubuwa 10 na Waya da ya Kamata ka Sansu

Abubuwa 10 da Ke Sa Kamshi da Dandanon Girki da Kuma Kyansa