Skip to content
Home » Yadda ake yoghurt (yagwat)

Yadda ake yoghurt (yagwat)

Yagwat dai abun Shane Wanda yake da dadi sosai amma sai dai kash bakowa ne yasan yadda zaiyi shi ba sai dai a sawo na kamfani.

Toh bawani abun wahala bane domin ko abune mai saukin gaske zaku iya yinshi acikin gida da dandano mai dadi, domin babu bukatar sai anfita ansawo

Ayau zamu koya maku yadda ake yinshi dakuma Kayan hadin da ake bukatar mutun ya tanada kamin yafara, ga Kayan hadin nan kamar haka;

Kayan hadin:

  • Madara
  • Fulebo
  • Suga
  • Ruwa
  • Kindirmo (nonon shanu)

Yadda ake hadawa

Yadda zakiyi shine dafarko zaki jika madara kamar minti talatin idan tajiku sai ki daura tukunya ki zuba kindirmo da wannan madarar jikakka ki sa ruwa kadan kita juyawa amma kar kisa wuta dayawa.

Bayan kinga tayi kauri-kauri sai ki juye sannan ki zuba suga da fulebo mai kanshin madara aciki ki motsa

Sai ki samu wuri kijuye aciki kisa acikin firic yayi sanyi.