Skip to content
Home » Yadda Ake Amfani da Pixel Lab App Wajen Gyaran Hoto

Yadda Ake Amfani da Pixel Lab App Wajen Gyaran Hoto

Yadda zaku yi amfani da manhajar pixellab wajen graphic design.
Pixellab application ne Wanda ya daɗe yana taka rawar gani wajen harkar Graphic Design wato zane, ma’anar Graphic design?


Graphic Design zane ne da ake tsara shi ta hanyar haɗa rubutu (text) da shapes da kuma hotuna, a tsara su ayi musu kwalliya don su bada launi mai kyau wannan shi ake cewa graphic design a gurguje bari mu fara bayani akan yadda za’a iya amfani da mA’anhajar pixellab.


Idan kuka ɗauko shi kuka shiga daga ciki tambarin wata A anan ake rubuta text idan zakuyi rubutu nan zaku shiga kuyi, zakuga wani plus sai ku shiga ku rubuta abun da kuke so sannan zaku iya sama text abubuwa kamar haka; Edit, Delete, Copy, To front, To back, Position, Relative position, size, color, texture, stroke, padding, opacity, rotate, mask,font, style, curve, background, align, spacing, line spacing, shadow, inner shadow, da dai sauransu to Yanzu zamu ɗauki ɗaya bayan ɗaya muyi magana akan su.

 1. edit yana amfani ne idan anyi text kuma ana so a goge wani abu ko a kara wani abu daga ciki.
 2. yana magana ne akan goge text ɗin gaba ɗaya
 3. copy shi kuma ana mai da ya zama double wato guda biyu ko fiye da haka
 4. to front shi yana magana ne idan anyi sosai jikin wata poster to Akwai wani suna dake kasa to za’a yi amfani da to front domin a mai doshi sama
  5.to back shi kuma yana magana akan a mai da shi kasa
 5. Position: idan za’a canzawa text wuri dashi ake amfani ko a kai shi dama ko haggu, sama ko kasa
 6. Relative position: shima kamar position yake amma sun da babban ci ana amfani dashi wajen mai do abu tsakiya dai dai ta sama ko ta kasa duk dashi ake amfani.
 7. Size: girman rubuta da kuke so ku sai ta dai dai da bukatar ku mafi aka sari yana zuwa a 40pixel
 8. Color: wato launuka d kuke bukata kuma color ya daga cikin abun da ke design yayi kyau.
 9. Texture: shi kuma wato jikin rubutun za’a sa hoto aciki kuma ba background zai yi ba.
 10. Stroke: shi kuma wani da ake sawa a karshen kowane design in Kuma wato wan layi ne.
 11. Padding: space ne na ciki wanda a cikin area ta text ɗin zaku ganshi
 12. Opacity: Ana amfani dashi wajen rage ma wani color ko a mai da abu yayi huri huri kamar dai yadda aka bakar leda yanzu kunga bata rufe abubuwa to kamar haka.
 13. Rotate: Ana amfani dashi wajen wajen canzawa abu Angle Kamar daga 30 ana iya mai dashi 90 ya kalli kudu maso arewa.
 14. Mask: ba fa Wanda mata ke ɓoye fuskar su dashi, wannan wani Abu ne da ake gutsire abu dashi.
 15. Font: font Yana daga cikin abun da ke nuna mutum ya iya design, saboda zaka yi poster ta ban tsoro to dole sai kayi amfani da font na rubutu wanda zai nuna na ban tsoro ne.
 16. Style: ana amfani dashi wajen sama text bold, ko italic ( wato rubutun nan kamar na yan mata mai lankwasa), underline
 17. Curve: idan za’ai mai da rubutu yayi bending to shi ake amfani dashi.
 18. Background: ai ina ga kowa ya san mi ake nufi da background Amma duk da haka bari mu ɗan yi magana akan shi kaɗan, duk wani wanda zai rufe bayan wani abu shi ake cema background misali idan kuka je registration na din card ba ana sa maku wani farin kyalle a bayan ku ba ida za’ai maku hoto, to kamar haka background yake shima a baya ake sa shi.
 19. Align: abu ne da ake amfani dashi wajen mai da rubutu ya fara daga tsakiya ko haggu ko dama.
 20. Spacing: shi kuma ana amfani dashi wajen sama letter ko word space wato sarari a tsakanin su.
 21. Line spacing: shi kuma space na tsakanin layi da layi.
 22. Shadow: Wato inuwa ana iya sama text ta nan.
 23. Inner shadow: shi kuma inuwa ta ciki
  A wuri na biyu zaku ga inda zaku hoto ko shapes dai sauransu idan kuna ku kware harkar Graphic Design kuna iya zuwa skyly.com.ng acan zaku koyi yadda ake haɗa logo, flyer, banner, letterhead, book cover da kuma yadda zaku sai ta size ko anje printing ba zaku samu matsala ba dai sauransu.