Skip to content
Home » Yadda ake fankasu (algaragi) na alkama

Yadda ake fankasu (algaragi) na alkama

Yau inshallah zani koya maku yadda ake fankasu na alkama wasu kuma nakiranshi da algaragi.

Shidai fankasu abincine na hausawa mai dadin ci Wanda akeyinshi da alkama kokuma fulawa.

Shidai wannan fankasu ana cinshi da miyoyi daban-daban misali miyar ja, taushe, gyada, agushi kokuma abun zaki kamar Zuma Dade sauransu ya danganta da irin miyar dakikeso kici dashi.

Kayan hadin da ake bukata wajen sarrafashi sine:

Kayan hadin

  • Alkama
  • Mai
  • Ruwa
  • Tsamiya
  • Kanwa
  • Gishiri

Yadda ake hadawa

Yadda ake shine zaki fara gyara alkama ki surfata kihece sannan kiwanketa kishanya tabushe.

Bayan tabushe sai anukata tayi laushi amma idan batayi laushi ba sai ki tankadeta ki zuba a wurin kwabi ki zuba gishiri kadan a garin sannan sai ki jika tsamiya ki zuba Kadan sai ki kara da ruwa sannan ki kwaba.

Kibarshi yayi kamar tsawon awa uku akulle zakiga yataso sosai sai ki jika kanwa ki zuba ruwan kanwan kadan a kwabin ki bubbugashi sosai.

Sannan sai ki Dora manki a wuta yayi zafi sai ki shafa mai a hannunki tayadda kwabin bai kama maki hannu.

Sai kirinka dibar kwabin kina budashi yadda zeyi fadi kina sawa a mai.

To idan kasan yayi ja sai ki rika juyawa ahaka har kigama duka.

To wanna algaragi kenan abincin hausawa saikuma munhadu a karo nagaba.