Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake peppered offals da yam (Kayan ciki da doya)

Yadda ake peppered offals da yam (Kayan ciki da doya)

To dafarkode ana bukatar kitanadi Kayan hadi kamar haka

Kayan hadin

 • Offals (yanciki)
 • Yam (doya)
 • Thyme
 • Curry
 • Koren tattasai
 • White pepper
 • Black pepper
 • Tarugu
 • Mai
 • Ruwa
 • Albasa
 • Gishiri
 • Citta/tafarnuwa
 • Bay leaf

Yadda zaki girka

Zaki fara wanke Kayan cikinki wato (offals) da ruwan zafi sufita sosai.

Sai ki zuba Kayan kamshi tareda albasa wato thyme, curry, black pepper, white pepper, gishiri, citta, tafarnuwa sai ruwa dai-dai gwargwado kimotsa

Sai kikulleshi yadan sulala.

To yanzu kuma saiki fera doyarki ki daddatsata kanana kiwanketa.

Sai kizubata atukunya kisa ruwa da gishiri tadahu.

Bayan doyarki tadahu, sai ki zuba mai acikin kasko ko tukunya tare da albasa yasoyu.

Saiki zuba wannan doyar dakika sulaka aciki tasoyu sannan kitsameta.

To bayan nan kuma sai ki dauko offals dinki dakika tanana (yanciki) suma kisoyasu acikin man.

Bayan kinsoyasu duka sai ki rage Manda kikayi amfani dashi kibar dede Wanda ze isheki sanwa.

Sannan ki zuba albasa, tarugu, citta/tafarnuwa, thyme, curry, cumin, bay leaf da pepper mix.

Kisoyasu natsawon minti biyar amma kada kisa wuta dayawa.

Bayan yasoyu sai ki zuba soyayyun offals dinki da doya sai koren tattasai ki motsa kamar tsawon minti biyu kingama.