Skip to content
Home » YADDA AKE SOBO (ZOBO)

YADDA AKE SOBO (ZOBO)

Ayau zani koya maku yadda ake hada sobo mai dadin gaske domin wannan ba kalar wanda kuka saba sha bane.

Sobo dai wasu yayan shukane da akasansu masu kalar ja wanda aka kasance ana sarrafa su ta hanyoyi da dama musanman ma wurin abunsha, domin shan sobo ma yana da anfani ga lafiyar dan adam kamar masu sikila.

Ayanzu zamuga kayan hadin da ake bukata domin hada lemun sobo (juice).

Kayan hadin

  • Sobo
  • Citta
  • Kananfari
  • Suga
  • Kokumba
  • Abarba kokuma bawonta
  • Fulebo mai kamshin abarba

Hausawa Site

Yadda ake hadawa

Zaki fara gyara sobonki ki aje a gefe sannan ki dauko abarba kifere bawon idan dashi zaki anfani sai ki samu citta danya kiwanketa kihada da kanunfari kidaka kokuma kimarkada, sannan sai ki dauko tukunyarki kizuba ruwa sannan ki dauko duk wadannan kayan hadin da kika gyara su markaden citta, sobo, bawon abarba kizuba sai ki kulle kibarshi ya dahu.

Bayan ya dahu sai ki juye shi cikin wuri mai yalwa kibar shi ya huce idan ya huce saiki samu rariyarki ki tace amma kinayi kina kara ruwa har sai jar kalar dusar sobon ta fita duka sannan sai ki samu kokumbarki kigur zata acikin kananun huji, idan kika gama sai ki dauko suganki da fulebo kizuba tare da kokumbar da kika gurza kimotsa, sannan kisa a firic idan yayi sanyi sai a sha.