Skip to content
Home » Yadda ake dambun shinkafa

Yadda ake dambun shinkafa

Dambu dai nadaya daga cikin abincin hausawa masu dadi Wanda aka iya yinshi da tsaba da dama misali kamar shinkafa, masara da sauransu.

Toh ayanzu zamuga kayan hadin da zamu tanada domin yin wannan dambu na shinkafa.

Kayan hadin:

  • Farar shinkafa
  • Mangyada
  • Albasa
  • Gyadar miya
  • Gishiri
  • Magi
  • Karas
  • Wake
  • Zogala ko kabeji
  • Nama

Yadda ake hadawa

Yadda zakiyi shine dafarko zaki fara samun farar shinkafa ki wanketa tas ki shanyata ta bushe, idan tabushe sai ki bada a barzo maki baccin an barzo sai ki samu rariya kitankade ta saiki dauki tsakin kijikashi da ruwa sannan kitsameta ki zuba a steamer (tukunyar dambu) sannan ki kunnan wuta.

Sannan kizo kigyara duk kayan hadin ki wato (ingredient) suzama acikin shiri ki aje, sai ki dauki namanki ki yankashi kanana kamar na fried rice sai ki tananashi ki juye sai ki hadashi da kayan hadin ki dakika gyara wuri daya. Idan tsakin ki na cikin tukunyar dambu ya turaru sai ki samu wuri mai fadi ki juye shi aciki sannan kikawo wadannan kayan hadin naki dakika gauraye su mai, nama, kabeji da sauransu ki zuba aciki ki motse shi sosai, sannan ki maidashi a madambaci ya dahu, idan yadahu zakiji yana tashin kamshi sosai sai ki sauke.