Skip to content
Home » Yadda ake yin man gashi

Yadda ake yin man gashi

Man Gashi


Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu jama’a muna fain cikin ziyartar wannan shafin mai albarka kuma a yau inshallahu zamu yi Magana ne akan yadda ake hada man gashi mai inganci wanda zai taimaka wajen kyaran gashi dama tsaftaceshi wanda na saidawa za’ay ko kuma na amfani a gida.

Domin gaskiya zamanin nan said a kula da kai da tsafta, kuma ma dama ay tsafta tana daga cikin addinin musulunci, wannan mai da zamu koya yanda ake yinshi kana ko kina iya yinshi don amfani ko kuma dan saydawa wanda muna sa ran duk wanda ya karanta ma inshallah ba wai kawai ya ringa yi ba a har ma ya samu sanaa da shi In ya inganta shi yadda ya kamata.

         To kafin mu shaga yadda ake hada aynafin shi man gashin da farko zamu yi Magana akan wadanne abubuwa ne ya kamata ka/ki samo na hada shi man gashin, kusan ana bukatar abubuwa kwara bakwai ne waddanda zamu lissafa kamar haka.

Abubuwan da ake bukata

Abuwan da zamu lissafa mutun zai iya zuwa kasuwa ya sawo su inshallah, sai dai ya danganta ga farashin da mutum ya same su da yanda zai sayar musamman ga wanda yak e karantawa do ya sayda to kar mu cika dumi bari muje gare su.

1.      Farafin oil : awo  shidda (farin sosai).
2.      Kala : za’a samo kala nemai narkewa sabo da ta narke cikin hadin sai a sata yadda ake so shi abun yay kalar.
3.      Starik acid : za’a zuba kashi daya bisa takwas 1/8 na abun da ake amfani ne dashi.
4.      Fetroleum jelly : za’a zuba awo hudu zuwa (4-6)  domin wannan shine tushen man, thosco sunan daya daga cikin ire iren shi fetroleum jelly da ake dasu da mutum ya je kasuwa ma inshallah zai same shi.
5.      Gilasarin : kashi daya ake so 1% sinadari ne mai sa kyalli da taushi.
6.      Farafin wax : shi ana sashi yadda ake so ne amma fa a sani yana sa bu ne yay karfi.
7.      Turare: shima turare ana sashi yanda ake so nae kawai.

Abubuwan da muka lissafa a sama sune kayan da za’a nemo a kasuwa, to yanzu bari muga yanda ake hada kayan ko sinadaran.


YANDA AKE HADAWA

Da farko za’a zuba awo shidda (6) na farafin oyal, sai a gauraya shi da kala, bayan ya gauraya sai kuma a tace shi.

Na Biyu za’a samu tikunya mai tsafta sai a zuba shi sannan a aza akan wuta, daga nan kuma sannan a sa kashi daya bisa takwas 1/8 na sitarik asid sai a motes su.

Na Ukku hada fetroleum jeli shikuma awo 4-6 a ciki, sai ajuya shi wato a motsa shi har sai ya narke.

Na Biyar  awannan matakin  shi kuma  za’a hada kashi daya 1% na gilasarin da farafin wax ( wato yadda ake so zaa sa , sai a motes su hadu soassai ) daga nan baccin an motes su sai a sauke a kasa, a bar turirin da ke tashi ya dan rage sanan daga bisani sai a zuba wato turare yanda ake kon kamshin ya kasance sai a motes su duka da turaren da aka zuba, to daga nan fa mashaallah an gama sai abunda ya rage shine a samu yan kwalaben da zaa zuba shi don a saida ko don amfani.

          To jama’a a nan ne muka zo wato aynafin karshen wannan post din muna fatan kunji dadinshi, kuma wanda yake da tambaya, kyara ko karin bayani sai ya rubuta a comment section kuma kuna iya subscribe da email dinku don samun sabbin post da mukai a wannan website mai albarku, mu dai kulun kokarinmu mu taimaka mu akasance tare da ku.