You are currently viewing Yadda zaka samu subscribers Masu Yawa a YouTube Channel

Yadda zaka samu subscribers Masu Yawa a YouTube Channel

Kamar yadda mukayi magana akan bude youtube channel a baya bayan ka gama hakan ka bude ka ma fara daura bidiyoyi wanda kake son a gani to abu nagaba shine ka samu subscribers wato wadanda zasu kalla.

Domin ba mai son a ce yana ta daura bidiyo babu yan kallo kaga abun ba ma’ana kenan to inshallahu  a wannan post din zan yi maka bayani akan yadda zaka kaucema ma wannan matsalar ta rashin yan kallo.

Mi ake Nufi da Subscribers a Youtube?

Subscribers suna nufin mutanen da suka ziyarci channel dinka suka kalli bidiyonka bayan sun kalla sai suka ji dadin abubuwan da kake dorawa to sai su danna maballin subscribe tare da karauraraw .

Kamar yadda kaji na ambaci karaurawa haka abun yake bawai wadda ake gani ba ina nufin ita wannan bayan an danna malin sai aka danna ta to da kayi sabuwar bidito youtube zai watsa ma duk wanda ya danna nan take.

Shikuma maballin duk wanda ya danna shi to duk lokacin da ka daura bidiyo zai gani idan ya shiga app din youtube a wayarsa ko kuma acomputer sa.

Kaga yana da kyau su hada biyu maballin da kuma karaurawar, to bayan nan bari mutafi akan matakan da zaka bi domin samun naka masu yawa.

Matakan da zaka bi

Ga wadansu daga cikin matakan da in ka kiyayayesu kuma ka bi su inshallahuzaka samu nasar.

Daura Bidiyo Mai kyau

Ba kawai abubuwan da kaga dama ba zaka rinka daurawa masu kau da marasa kau ba wannan babbar matsala ce wadda takan iya ja maka rashin yan kallon gaba daya a kafar.

Zaka ringa daura abubuwa ne masu kyau masu kayatar da yan kallo  tare da ja masu hanakali yadda kullun zasu ringa kallon abubuwanka.

Kamar yadda nayi magana a baya akan Kayan aikin Youtube to yana da kyau ka tanadi abubuwan gyarn bidoyo na daukar bidiyon ma ita kanta da sauransu wannan shi yake taimakawa wajen kayatar da yan kallo.

Wani abu kuma mai hahimmanci shine ka rika sama bidiyonka hoton da zai ja hankalin yan kallo wanda da sun gani zasu yi sauri su danna su kalla, nasan in kana shiga youtube kana ganin irin hakan.

 

Watsawa a Kafar Sada Zumunta

Abu mai matukar amfani na biyu bayan wanda na ambata maka a baya shine sai kuma kasan yadda zaka rinka watsawa a cikin kafafen sada zumunta yadda zaka ja abokananka da ma sauransu.

kafar sada zumunta

Kafafen sada zumunta irinsu Facebook, Whattsapp, tiktok, da instagram suna bari a watsa link a cikin su kaga wannan dama ce wadda ka samu mai girma.

Amfanin wannan baya ga ka samu yan kallo kawai yana kuma taimakwa wajen yada yada bidiyon ka da ta burge wani ya tura zuwa ga sauran mutane.

Sai dai kuma akwai wani abu mauhimmi da ya kamata ka sani game da yan kafafen sada zumunta suna son ka  amfanar da su sosai kafin ka samu wani ya tura maka abunda ka dora a sama.

Tunatar da Yan kallo

Abu na gaba kuma shine karika fadama yan kallonka cewar suyi subscribe tare da danna maka karaurawa ta yadda da ka dora sabuwar bidiyo zasu gani.

Wannan kana iya yinshi ne a farkon bidiyonka da kuma karshe amma ni a shawara ta ka sa duka a farkon da karshen domin idn kasa a farko babu a karshen suna iya mantawa su fita hakanan.

To kaga duka suna da mahimmanci.

Yawan Daurawa

Tabbas ko shakka babu yawan dora sabuwar bidiyo a youtube yana taimaka maka sosai kusan hanyoyi masu yawam kamar haka.

Na farko dai zaka rinka yawan samun masu kallon video dinka wanda hakan yana taimakawa wajen samun kudi a youtube.

Karanta : Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Na Biyu kuma shine su irin wadannan manhajoji na zamani ana sa ma su fasahar da take gane sa yawan mabiya su rika lura da wadanda suke bi.

A nan ina nufin idan kana yawa dorawa to zakaga anfi yawan watsama wadanda suka yi maka subscribe ba kamar idan baka sawa ba zaka ga yan kallon ba yawa, to kaga dorawa akai akai yana taimakaw shima.

Abu na ukku kuma shine idan kana yin hakan zaka kamfanin zai rinka ba wadanda basu tare da kai shawararw su kalla bidiyonka daga nan kaga suna iya yin subscribe