You are currently viewing Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya

Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya

Ita wannnan sana’a ta gyaran waya abu ce mai matukat amfani wadda yanxu ake bukatar ta sosai saboda kowa a yanxu yana da waya kuma wayoyin da wuri suke saurin samun matsala.

Idan suka samu matsala sai dole an nemi mai gyara an kaimashi ya kyara a biyashi kudi kuma ya danganta iya tsadan wayar mafi yawanci iya yadda ake yanaka, kudin shiyasa a wannan post din namu na yau muka ce bari muyi magna a kan ta da abubuwan da ta kunsa.

Abunda Gyaran waya ya kunsa

To ita dai wannnan sana’ar ta gyaran waya ta kunshi abub uwan da suka shafi gyarama mutum wayar sa ta salulu daga wata matsala da ta samu zuwa tayi  lafiya kuma ana yinsa ne wani lokacin nan take idan mutum ya kawo ka gyara masa.

Ko kuma bayan wani lokacin idan an nemo ko an sawo wani bangaren da ake nema na wayar sai a sa a gyara ita wayara amma da sharadin bayan an gyara ake biyan kudin gyaran wayar saboda ba mai son yayi asara biyu abu bai gyaru ba anyi asara shi haka makudin.

Akwai bangarori da dama da suke samun matsala wadanda ake sakewa a cikin waya wanda mai gayar kodai ya gyara su ko kuma ya sake su gabakidaya, ga kuma wasu daga cikinsu kamara haka:

Karanta: Sana’ar Communication da Abubuwan da Suka Shafe ta

Abubuwan da Ake gyarawa

Wadannan abubuwan da zan lissafa a kasa sune ya kamata a ce ka san yadda zaka iya gyarasu mafi karancin iya gyara a matsinka na mai gyaran waya saboda ana yawan samun masu kawo matsalolin da suka shafe su kuma ana son ka gyara da inganci idan kana son a dawo maka.

  • Canza Screen
  • Canza Mouse
  • Canza Speakers
  • Sanya Screen Guard
  • Chanza gindin caji
  • Canza wurin layin SIM

Abubuwan da muka ambata a sama suna idan ka iya su kana ma iya fara ita sana’aar amma yana da kyau ka sani akwai sauran abubuwa kamar ko ince matsalolo na cikin waya wanda suma ya kamata a ce ka iya su wasunsu ana amfani da computer shiyasa yana da kyau ka iya computer, kamar su flashing din waya dole sai kana da com[puter zaka iya yinsa.

karanta: Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware