Duaknci sana’a ce ta hausawa wadda suka dade suna kuma suke gada kaka da kakannin domin samun abun dogaro da kai wanda tana daya daga cikin manyan sana’oin hannu na gargajiya da aka sani hausawa suna yi
kamar dai yadda aka sani cewar kowace sana’a tana kunshe ne da abubuwa kala daban daban kama daga kayan da ake amfani dasu a sarrafa da kuma kayan aikinta itama dukanci haka take kuma zamuyi bayani akan mi ake nufi da dukanci ya ake kiran mai yin sana’ar dukanci dama amfaninta.
Table of Contents
Ma’anar Sana’ar Dukanci
Dukanci Sana’a ce ta hausawa mai yinta kuma a hausance a ana kiranshi ne da Baduku, yana amfani da fata ne ya sarrafa ta zuwa abubuwan mutane zasu yi amfani ko kuma muce ya kirkira kayan ma’aikaci wanda a’a rika amfani nda su kamar irinsu jikka, takalmi, rariya abub uwan laya da sauransu.
Idan akace baduku babban abunda yake sarrafawa shine fata ita ce yake canzama launi ko kuma ya juyata zuwa ga abu mai amfani ga mutane kamar dai yadda muka ambata a baya.
Karanta:
Kayan Aikin da ake amfani da su
Kamar dai yadda ake sani cewar kowane mai wata sana’a ta hannu yana da kayan ma’akacinsa to sana’nar dukanci itama ga wasu daga cikin kayan da aka fi amfani da su wajen aiyukanta.
- Fata
- Allura
- Wukar Icce
- Tuwo
- Kokon Gigimya
- Zare (Musamman zaren lilo)
- Icce
- Garura
- Almakashi
Ga bayaninsu kamar haka
Fata
fata a dukanci kusan itace babban abun da ake sarrafawa wanda baduku yake amfani da da abubuwa daban daban wajen samar da sabbin abubuwa ko kuma gyara wadanda suka lalace kamar su jikkuna, takalma da sauransu.
Allura
Baduku yana amfani da allura ne wajen tsira zare dimin samun damar matse fata ko kuma ya dinke mahadar wurare biyu na fata wadda shima yana da yanayin allurarshi.
Wukar Icce
Wukar icce tana yin aiki ne kamar na ace a shafa wani abu mai kala to da ita za’a yi amfani akwai wani abu da ake shaafawa a fatar tayi kyau wanda ake kira da garura.
Tuwo
Suna amfanine da tuwa a matsayin gam abunda zai manne fata da sauran abubuwa a waje daya domin su matse bayan sun sha isaka su tada tsayin abu lafiyayye.
Kokon Gigimya
Kokon giginya shine kamar wurin da ake zuba tuwon a ajiyeshi ma’ana kamar amfanin dai da roba takeyi a adana abubuwa a cikinta to shima haka yake kwallon giginya ne ake fasawa a raba shi gida biyu ayi amfani da baren a matsayin mazubi mazubi haka.
Zare (Musamman zaren lilo)
Zare ana mafani da shi tare da allura domin a dinke fata ko ayi facin inda ya bule ko ya samu matsa a cikin aikin dukanci.
Icce
yana zama a matsayin abunda za’a daura ayi aikin a samanshi a dinke wani abu ko kuma a gyara shi
Garura
Abu ce kamar tawadda a misalce ma’ana shafa ma fata tayi kyau ta kuma yi kyalli sosai yadda ata ba mai kallo sha’a wa ana amfani da wukar icce wajen debo ta a shafa ko a sarrafa ta.
Almakashi
Baduku yana amfani da almakashi a matsayin abun da zai rika datsawa ko kuma ya raba fata ko ma ya juyata tyadda yaga dama kamar dai yadda tela shima yake amfani da almakashi.
Abubuwan da Baduku ke hadawa
Akwai abubuwa da yawa da baduku ke hadawa wanda kuma gasu kamar haka a lissafe
- Takalman Fata
- Jikkunan fata
- Rariya
- Gyaran takalma
- Abubuwan laya
Amfanin Dukanci ga Hausawa
Sana’ar Dukanci nada matukar amfani saboda kusan a wancen lokacin babu wani abu da aka fi amfani da shi kamar fata sai kuma abubuwan da suka shafi icce ko kore a matsaayin kayan ma’akaci.
Karanta:
Wasannin Kasar Hausa na gargajiya
Sana’oin Gargajiya: Manyan Sanaoin Gargajiya na Kasar Hausa wanda Hausawa Ke yi
Ga kuma wasu muhimman rawar da wannan sana’a ta taka a kasar hausa musamman a lokacin da
- Ana Kera ko kuma samar da abubuwan amfani a wancen lokacin na fata tunda babu roba.
- Samar da hanyar dogaro da kai ga mutane.
- Samun damar gyara abubuwan da suka lalace kamar su takalma da jikka da sauransu.
- Kirkiro abubuwa daban daban na fata domin amfanin alummna.
- Habbaka tattalin arziki ta hanyar amfani da jemammar fata
Abubuwan da muka amfaba a sama suna dakga cikin amfanin wannan sana’a a dukanci babbar rawa da ateke takawa.
Karanta:
Skyly: Ƙungiyar Koyon Sana’o’in Zamani Domin Dogaro da Kai
Dogaro da Kai: Shawarwari 5 Masu Mahimmanci ga Matasa domin Dogaro da Kai:
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin