Skip to content
Home » Dogaro da Kai: Shawarwari 5 Masu Mahimmanci ga Matasa domin Dogaro da Kai:

Dogaro da Kai: Shawarwari 5 Masu Mahimmanci ga Matasa domin Dogaro da Kai:

A cikin wannan zamani da muke ciki dogaro da kai abu ne wanda ya wajaba musamman a wajan matasa, wanda shiyasa har kullun matasa suke neman ya ake dogaro da kai ko ya ake fara kasuwanci ko kuma ma ya ake fara sana’a domin inba da haka ba tunani canzawa yake a fada abubuwan da ba’a so kamar maula ko aiukan asha.

A cikin wannan rubutun namu na yau zamuyim magana akan yadda hanyoyin da matasa z\asu bi domin su dogara da kansu ta hanyar sana’a har su kafa wani.

Dogaro da Kai ga Matasa

A kasashen da suka cigaba zaka samu matasansu sun jajirce wajen aiyuka kala kala suna kokari kullun wajen kirkiro sabbin abubuwa wanda da haka ne ake samun cigaba.

Manyan kasashe kamar irinsu china da Amerika kusan hanyoyin da mutane suke samun kudi fiye da kashi 90% cikin daga masanaantu ne wanda ya hada da kamfunnan, kanan da matsakaitan sana’oi da sauransu.

hakan ne ya taimakawa kasar wajen rage matasa marasa aikin yi da yan zaman banza wanda hakan yakan taimaka wajen rage laifuffuka dayawa a cikin kasa.

A cikin kasashe irin Nigeri idan ka kula garuruwan da suka fi yawan kamfunna anfi samun saurin aikin yi kuma kudade sunfi wadatuwa a wurin saboda yadda aikin yi yafi yawa bisa ga idan aka kwatanta da garuruwan da yawanci gwamnati suka dogara akansu.

 

Ilimin Karatu da Rubutu

A karoon farko samun background ko ince ilimin farko mai inganci abu ne da yake taimakawa sosai saboda ta shine mutum zai iya fahimtar karanta wani abu inya gani.

Wadannan ilimomin yawanci mu a nan fannin hausawa  kusan fahimtar yare biyu yana taimakawa duka wanda sune turanci da kuma larabci sai kuma akwai bukatar ace mutum yana da ilimin lissafi

Duk wannan a lokacin yarinta aka fi bukatarsu ace mutum yana da su kuma ma banda wannan an bukatar mutum ace yana da wayewa ta wani ilimi na daban kamar na computer da sauran abubuwan kimiyya da fasa koda kadan ne

Buri ko Mafarkin Rayuwa

A farko yara yawanci ana dora su ne akan abubuwan da suke muradi ne idan sun girma misali in ka girma mi kake son ka zama, wannan shine abu mai mahimmanci.

Tun mutum na yaro koma inya girma ana son yakance yana da mafarkin abunda yake son ya zama wanda yake jin dadin yinsa ba tare da sarewa kuma yake cigaba da yinsa.

Hakan wasu kasahse da yawa musamman wadanda suke cigaba suka zarce mu yara zai girma da mafarkin abunda yake son zama kaga cikin unguwa har mai kula dashi ke akwai wato mentor

Ilimin Sana’ar (Skills)

Daga nan kuma anson mutum bayan ya samu ilimin na farko ya kasance idan ya girma ya taimaka mashi mashi a fannin koyon ilimin sana’a..

Musamman a irin wannan zamani da muke cike da abubuwa na yanar gizo wanda fannin internet ga komai kusan za’a ce da wuya ka duba baka samu bayani akanshi ba.

To matasa akwai bukatar ace yazamana suna amfani da ilimin backround dinsu suna research kan abubuwan da suke son su cimmawa a rayuwarsu.

Fara Sana’a

Fara sana’a ko kasuwanci yawanci ya rabu gida biyu kodai mutum ya kafa nasa kasuwancin ko kuma yayi aiki a karkashin wani amma ya kafa nashi yafi.

saidai kuma a yanayin matasa saboda karashin sanin abubuwa rayuwa da kuma kudi abunda aka fi so shine ka fara samun wanda zai saka hanya saboda inkai daya ne kana iya dadewa kana yi sannan ka gane amma idan da wani yana iya nuna ma hanya mai sauki wjen yin  abubuwa.

Karanta:

Sana’oin Zamani 10 Masu Saukin Yi ga Mazauna Kauye ko Karkara

Fasahar ChatGPT da Yadda take

Habbaka Sana’ar

Bayan fara kasuwanci kokuma sana’a abu mai mahimmaci na gaba kuma shine matakan habbaka ta ta yadda zata girmama ta zama babba ba maison ya fara kasuwanci ace kullun yan a wuri daya.

Don haka kokarin habbakata da karamata jari gami da inganta ta shine abu mai mahimmaci da duk wani matashi mai neman sana’a ya kamata ya rika tunani a kullun.

Shiyasa a kasashen da suka cigaba da sun fara wani kasuwanci burinsu shine ya za’ayi ya kai matakin zuba jari yadda mutrane da yawa zasu zuba jari ya zama babba zuwa billion dolar company, hakan yana taimakawa sosai.

Karanta:

Kasuwancin Online: Yadda ake amfani da fasahar yanar gizo(internet) a habbaka kasuwanci

CIKAKKEN BAYANI AKAN SAMUN KUDI ONLINE TA FREELANCING

Fasahar Biogas: Bayani akan Samuwar Gas daga Shara ko Bola

 

A tuntubemu akwai group da muke hadawa domin shiga