Skip to content
Home » Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata

Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata

Yanzu hain da ake ciki mafi yawancin mutane da yawa na jajircewa suna yin abubuwa da kansu musamman fannin da ya shafi kekere kere na abubuwa daban daban wanda yazu kasashe masu tasowa irinsu Nigeria an fara samun irn wannan cigaban, hakan yana da nasaba ne ta sanadiyar yadda mutane da yawa suka fada halin rashin aikin yi da sauransu.

Hakan ne yasa a cikin wannan post namu na yau naga bari inyi tskaci akan wannan muhimmin abun saboda yadda yake da matukar amfani ga alumma saboda wani yanada da fasahar amma baisan ina zai samo kayan ba,wani kuma yana da tunanin amma bai san ya zai fara ba duka har ma wanda bayada irn wannan tunanin zamu tabo a ciki da inshallahu.

Dalilin da Ya sa Ake Bukatar KirKiro Abubuwa

Kamar yadda nasha fada a baya na daya daaga cikin babban daiin da yasa ake bukatar kirkiro wani abu shine domin habbaka tattalin arziki da sawwaka ma mutane, kuma abu ne wanda mutum zai taimaki kansa misai yanzu wani ya karanci engineering idan yayi amfani da ilimin da ya samu yayi kokarin kirkira wani abu ya taimaki mutane da yawa.

Hakan yana taimakawa daga nan wani lokacin daga shi daya abun yana iya girma ya koma su dayawa suke aiki karkashin wannan kamfani saboda duka turawan nan mayan kamfunna irnsu Google, Facebook da sauransu irn na hada Waya Iphon da sauransu sun fara ne daga karamin jari daga kirkira, baso ce sai gwamnatin kasarsu ta basu aiki ba kuma gashi sun samu nasara.

kere kere da inda ake samun kayan

Matakan da Ake bi Domin Gina Fasahar

Bawai kawai turawa keda tunanin kirkiro sabon abu ba ko sukeda kokari aa mutane da yawa suna da shi har namu na africa sai dai ko asamu rashin jajircewa da goyan baya daga mutanen namu kuma yanzu da yawam mutane sun fara kokarin  gina kamfunnan masu samar da abubuwa kala daban daban to idan kanason hada wani abu ga wasu matakai masu amfani da ya kamata ace ka bi da zasu taimaka.

Samun Idea Mai kyau

Farko dai ka tsaya kayi tunani a fannin da kafi so kafi kwareawa kaga cewa ina mutane ke fukantar wata matsala kuma ta wace hanya zaka bi ka gyara musu ita ma’ana mi suke bukata da basu da shi ko kuma yake bukatar gyara shin misali keken wutar lantarki kokuma wata fitila ce zaka samar.

Ka tsaya ka natsu iaya karfin tunaninka na idea iya yadda zakayi saurin cin nasara idana bun ya tabbata, kada kace tun farko bani iyawa ka tsaya ka yi tuananin don taka rawa ga alummarka.

Research na Iiminta

Abu kuma na biyu shine kanada bukatar bincike akan abun kamar yadda muakayi bayani akan Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo munyi bayani yadda ake amfani da internet domin bincike saboda yanzu ilimi yayi yawa kusan komi kakenson hadawa gashi nan himmarka kawai ake so da dagewa da maida hankali sosai a kansa.

Irinsu Kafar Youtube  da google babbar makami ne da yake taimakawa sosai saboda mutane da yawa suna kokari dora abubuwa da dama a sama a nan ana iya koyama kuma ma har ka samu inda zaka iya sayen abunda aka koyar da kai cikin sauki ba tare da wahala ba.

Inda zaka samu kayan

Abu na gaba kayan hadin abubuwan yin research da iya abun shine farko bayan nan yadda zaka tattra abubuwan yanzu kusan Allah ya kawo mu wani lokaci da muka samu kanmu kusan duniyar a dunkule kana gida kana iya sayen abubuwa a kawo maka har gida.

Ko abu babu shi a gida nigeria kar ka damu kana iya kokari kaga cewa ka duba onine kayi order koda daga china ne ta hanyar su ali express, jumia, amazon da sauran wuraren onine da ake saida akaya a kawo maka gida.

Yanayin Kudin da Kake Bukata

Daga cikin abu mai mahimmanci kuma shine jari yanayain budget dinda kake bukata gabakidaya shima wannana abu ne mai amfani kila ma kana bukatar ka samu wuri to koda daga shago ne kana iya farawa koda kau na cikin gida ne don Amozon, Google da sauransu duk daga garage suka fara karanta tarihi kaji.

A karshe muana kokarin karfafa alummar mu ne su zama masu tunanin mai kyau kayi aikin da zaka iya taimakawa alummarka da zagayeka hakan shine rayuwa,

Karanta:

Yadda Ake Amfani da WPS Software

Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo