You are currently viewing Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo

Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo

Shi kana so kaza ma dilalin yanar gizo?

ko yaushe fa mutane suna kai tunanin su nesa ba kusa ba kan batun magana akan affliate marketing ko irin su freelancingfreelancing kokuma duk batun abunda ya shafi harkokin sana’o’in internet wato de abunda ake cewa “magani a gonar yaro; wlh yawan tambayar irin sana’ar da mutum zai fara a internet tana bani mamaki bayan ni a duniya banga wata kasuwar da ba’a iya cike guraben taɓa kamar sana’ar ta internet koda akwai ni ilimi da tunani na basu hango ta ba, wallahi duk lokacin da na tsananta bincike akan harkokin sana’o’in internet da samun kuɗi a online nakan ƙara hararo girman Allah Subhanahu wata’ala ne a zuciya ta domin shine “arrazaƙu” internet fa cike yake da fassarar ayoyin Alkur’ani mai girma idan mutum yayi tun-tun-tuni da nazari, a rayuwa ta ban taɓa ganin wani abu da tunani na be iya kaiwa ƙarshen sa ba sama da internet ikon Allah!

Wallahi bana shakkar rubuta littafi mai taken sana’o’i dubu a internet nayi imanin cewar a lokacin da na gama rubuta guda dubu ɗin kuma zan ci karo da wasu sababbin da sai naji a raina ai yakamata ace na rubuta su nima fa yanzu nake koyo da bincike ina kuma ga masana manya?

rashin bincike da bin diddigi dakuma faɗaɗa tunani shine kawai matsalar mu sai kuma rashin jurewa wahala a harkar.

duk wannan fa ina shimfiɗa ne akan dillalin yanar gizo kun san me hakan yake nufi?

ai kun san dillalai de ko? wanda suke dillancin gidaje ko shaguna ko wasu abubuwan a kasuwannin mu na gargajiya da muka saba dasu.

Wanene Dillalinn Yanar Gizo?

Dillalin yanar gizo-gizo shine Mutum ya ɗauki gaɓarar tallata siye da siyarwa na Digital Products da kuma digital services anan ma fa an kuma ko? domin wasu zasu ce menene kuma Digital products da services amma kuma zance baka bibiyar rubutu na kenan ko wani mai yin rubutu a wannan ɓangaren.

Digital products sun haɗa da irin su facebook page, groups, account ko twitter handle, ko Instagram ko Tiktok duka fa wannan abubuwan ana iya siyar dasu kuma akwai abunda ake ƙira entrepreneurship pillars wato mai neman siya da mai neman siyarwa da kuma abunda za’a siyar to me yayi saura? dillalin yanar gizo-gizo mana eh! Haka ne fa ƙwarai kuwa domin mai neman siya yana nema mai siyarwa a kasuwanci, mai neman siyarwa yana neman mai neman siya, dillalin kuma zai zama mai haɗa wa tsakanin mai siya da mai siyarwa yanzu dan Allah kana buƙatar wata Rijista ko izinin wani dan fara wannan? Kokuma kawai kana online ne kana jiran topic a tattauna wanda baze amfane ka ba? wani topic ɗinma akwai saɓawa Allah aciki fa mu lura!

yanzu dukkan mutanen nan da suke hada-hadar siyan Pi da core da kuma social media handle kala-kala zanen fuska sukafi ka kokuma su da wannan aka halicce su? duk fa fafutuka ce kawai dayawa sun cimma nasarorin rayuwa a yayin da wasu kuma suke ta tambayar tayaya zasu fara samun kuɗi a yanar gizo-gizo bayan ga dillalin yanar gizo-gizo da ko wata ƙwarewa ta musamman ma baka buƙata domin farawa.

Dillalin yanar gizo-gizo kai tsaye zaka tsunduma ne neman abun siyarwa da kuma abun siye ta hanyar shiga tsakani kaima ka samu naka kason ta hanyar halal kuma eh halal na dukkanin wani digital products da services.

Abubuwan da kake buƙata dan zama dillalin yanar gizo

kawai wayar Android sai kuma ƙarfin zuciya da juriya da sanin cewa ba yau zaka fara kuma kafara nasara yau ba; akwai sana’ar dana fara dafarko ina samun ₦200 kacal a rana ammafa yanzu ko wata ba’a yi ba ina samun ₦2,000 a rana kunyi mamakin yadda ₦200 ta koma ₦2,000 ko? to ba komai bane illa jurewa akan fafutaka da ƙarfin zuciya da kauda kai akan abunda za’a faɗa akan ka.

Bayan wayar Android kawai abunda kuke buƙata fa shine sanin irin abubuwan da ake tsaka da kasuwancin su ta hanyar neman mai siya dakuma mai siyarwa misali a yanzu haka ana siyan PI NETWORK kuma duk masu siyan nan dillalan yanar gizo-gizo ne fa domin kuwa ba dafawa sukeyi suna ci ba suma in sun siya siyarwa sukeyi zuwa gaba haka kuma zaku tsunduma cikin irin wadannan kasusuwan ci domin a dama daku kuma duk yawan ku kowanne rabon sa zai samu zaku na gani a lokuta dayawa fa wasu suna tallata siyar da page nasu yayinda wasu kuma suke tallata neman siya yanzu anan.
Lokaci yayi da ya kamata kufara sanar dilalin yanar gizo.

Karanta:

Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin

Forex Trade: Bayanin Forex Trade da Yadda ake yinsa