Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake miyar yalo

Yadda ake miyar yalo

Ayau zani koya maku yadda zakuyi miyar yalo mai dadin gaske. Sannan kuma ita wannan miyar zaku iya cin abinci kala-kala da ita kamar farar shinkafa, alkubus, algaragi da sauransu.

Kayan hadin da ake bukata ki tanada sune:

Kayan hadi

  • Manja
  • Albasa
  • Tumatur
  • Busashshen kifi
  • Yalo
  • Seasoning
  • Pepper mix (cefane)
  • Gishiri
  • Alayyahu
  • Ruwa

Yadda ake hadawa

Dafarko zaki fara yanka tumatur, albasa da yalo kanana ba manyaba.

sai ki soya manja yasoyu sannan ki zuba albasa, tumatur dakuma pepper mix (markadadden cefane) kisoyasu.

Sai ki zuba busashshen kifi da yalo saikuma seasoning tareda gishiri kimotsa na yan sakanni.

Sannan sai ki zuba alayyahu tareda ruwa amma ruwan kadan, sai ki rufeshi nadan lokaci kadan yadahu.

Ammafa base ruwan sunyi kauri ba, shikenan kingama.