Skip to content
Home ┬╗ Sirrin girki

Sirrin girki

Akace de girki adon mace, tabbas kidage kisan wadannan dabaru domin zasu temaka miki sosai a wurin girkinki.

Wadannan abubuwa sune:

1) Idan kikayi kuskure gishiri yayi yawa a abincinki ko a miya, abinda zakiyi shine *ki fere dankali kijefa a ciki domin dankalin zai shanye gishirin*.

2) Alokacinda abincinki ya kone yakeyin kauri *kisamu biredi mai yanka-yanka guda daya kidora akan abincin, biredin zai nade kaurin. Ammafa kiyi hankali karki kankaro wajen daya kone yayinda kike dibar abinci*.

3) Idan kuma miyar tumatur kikeyi ta kone, *zaki sauke ki sauya tukunya sannan kina kara suga kadan-kadan har sai dandanonshi na kaurin yatafi*.

4) Idan Maine yayi yawa acikin miya ,yadda zaki shine *kijefa kankara karama zakiga ta janyo man guri daya sai kawai ki kwashe*.

5) Idan bakyasan dankalin da kika ajiye a cikin buhu yafara tsiro, *saka tuffah guda daya acikin buhun*.

6) Karki ajiye ayaba guri daya da sauran Kayan itace *domin tana sakin wani iska mai sasu nuna da wuri Wanda zai iya haifar da saurin lalacewa*.

7) Idan gishirinki yafara curewa saboda danshi, *kijefa kwayoyin shinkafa a ciki zasu shanye damshin*.

8) Idan kika hada kofunan gilasai biyu kika kasa rabasu, *kisaka kankara acikin nasaman, nakasan kuma kuma kisakashi acikin ruwan dumi, na kasan zai fadada nasaman yatsuke Wanda zai saukaka rabasu*.

9) Kar kiyi ajiyar lemun tsami da tumatur a firij *domin sanyi narage masu kamshi da dandano*.

10) Idan tukunyar aluminiyan kike amfani da ita kuma tafara kodewa, nasan kinsan yadda zaki wanke bayan yayi sheki, toh amma acikin fa? abunda zakiyi shine *ki zuba bawon tuffa aciki daruwa ki dafa zai rage kodewar*.

11) Idan kinaso kikara amfani da man da kikayi suya dashi kuma bakyasan kamshin abunda kika soya yafito, *to ki soya danyar citta kadan aciki zai kawar da kamshin*.

12) Idan cinnaku sun addabeki a kicin, *kinemi hudar dasuke fitowa kishafe basilin a wurin ba zasu iya tsallakewa ba.

Idan kuma ta karkashin kofa suke shigowa, to kija layi da alli a gurin shima bazasu ketare ba*.