Skip to content
Home » Yadda ake kunun gyada

Yadda ake kunun gyada

Kunun gyada na daya daga cikin kunnukan hausawa masu dadi, wannan kunu Nada dadin sha sosai musamman ma idan yanada zafi.

Ayanzu zani lissafo kayan hadin da ake bukata wajenyi.

Kayan hadin:

  • Gyada
  • Shinkafar tuwo
  • Suga
  • Lemun tsami
  • Madara

Yadda ake hadawa

Yadda ake hadawa shine dafarko za’a fara gyara shinkafar tuwo awanketa a rege tafita tas, sannan sai a samu gyada itama agyarata, baccin angama gyarawa duka sai adoko wannan gyararrar shinkafar ahada da gyada ajika.

Bayan sun jiku sai asa acikin bulanda a markada, idan ya markadu sai a samu mataci a tace sannan a daura tukunya a wuta a zuba tataccen ruwan aciki adunga juyawa harsai yakai kaurin da ake so sannan ajuye sai a samu suga, madara da lemun tsami asa amotsa sannan asha.