You are currently viewing HANYOYIN DA AKE MAGANCE KURAJEN FUSKA

HANYOYIN DA AKE MAGANCE KURAJEN FUSKA

  1. Kuraje da rashes a fuska na daga cikin matsalolin fata da suka fi yawan damun mutane musamman matasa da kuma mata. Wannan matsala na shafar kwanciyar hankali da kwarin gwiwa, musamman idan fuska ce ke dauke da su, domin fuska ita ce abun da mutane ke kalla da farko. Sau da yawa, mutane na amfani da magungunan zamani masu sinadarai domin su magance kuraje ko rashes, amma galibin su kan bar illa ga fata ko su ƙara dagula lamarin. Wannan rubutu zai bayyana hanyoyin da za a bi wajen kula da fatar fuska da kuraje da rashes ta hanyar amfani da kayan gida masu sauki, na dabi’a kuma marasa illa.

Menene Kuraje da Rashes?

Kuraje su ne ƙananan kumburi ko tabo a fata da ke cike da sinadaran fata da kwayoyin cuta (pus), suna fitowa ne sakamakon toshewar matatun mai a fata (sebaceous glands) ko canjin hormone. Rashes kuma na nufin ja ko karcewa ko kumburi a wani bangare na fata wanda ke faruwa sakamakon rashin lafiyar fata, rashin tsafta, ko wani abu da ya fusata fata. Duka matsalolin suna bukatar kulawa mai tsari da lura sosai.

Abubuwan Da Ke Haddasa Kuraje Da Rashes

  • Canjin hormone musamman lokacin balaga ko haila
  • Yawan amfani da kayan kwalliya marasa inganci
  • Rashin tsafta ko wanke fuska sau da dama a rana
  • Yawan cin abinci mai mai ko sukari
  • Tashin hankali (stress)
  • Rashin barci mai kyau
  • Rashin shan ruwa sosai
  • Allergy daga sinadarai, sabulu ko abinci

Yadda Zaka Magance Kuraje da Rashes a Gida – Hanyoyi 10 Masu Sauƙi

1. Aloe Vera (Zabon Gwanda)

Aloe vera na dauke da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cuta da rage kumburi. Yana sanyaya fata kuma yana taimakawa wajen rage ja da karcewa. Domin amfani da shi, ka fere ganyen aloe vera, ka zare gel din, ka shafa kai tsaye a fuska da daddare, ka barshi na mintuna 20 zuwa 30 kafin a wanke.

2. Zuma da Lemo

Zuma na da antibacterial properties, yana magance kwayoyin cuta. Lemon tsami kuma yana rage mai a fata. Haɗa cokali 1 na zuma da ruwan lemo kadan, shafa a fuska, a barshi mintuna 15, sannan a wanke da ruwa mai dumi.

3. Kurkur (Turmeric) da Madara

Kurkur na rage kumburi da kuma inganta lafiyar fata. Haɗa turmeric da madara sai a shafa a fuska kamar mask, a barshi mintuna 20, sannan a wanke. Ana iya yin hakan sau 2 a mako.

4. Cucumber (Kabeji)

Yanka cucumber ko a markada shi, a manna a fuska mintuna 15, yana rage zafi, kumburi da karcewa. Zai kuma sanyaya fata sosai.

5. Ruwan Ganyen Neem (Dogon Yaro)

Ruwan ganyen neem na da kwayoyin magani masu matukar karfi wajen yakar kuraje da rashes. Ka tafasa ganyen, sai ka barshi ya huce ka dinga wanke fuska da ruwan ko ka shafa da auduga.

6. Oatmeal Mask

Oatmeal na cire mataccen fata da kawar da redness. Nikakken oatmeal a hade da madara ko yogurt ana shafa a fuska kamar mask, a barshi mintuna 15 zuwa 20.

7. Ice Pack (Kankara)

Kankara na rage kumburi da ja. A lullube kankara da zane mai tsabta, a shafa a fuska na mintuna 5. Amma a guji amfani da ita kai tsaye ba tare da kariya ba.

8. Shan Ruwa da Yawan Danshi

Shan ruwa akalla kofi 8 a rana yana taimakawa wajen fitar da gubobi daga jiki da samar da lafiyar fata. Hakanan, a dinga amfani da moisturizer maras sinadarin mai.

9. Gujewa Taɓa Fuska da Hannu Mai Doya

Yawancin cututtuka da ke yaduwa a fuska na faruwa ne ta hanyar hannu. A guji matse kuraje ko taɓa fuska akai-akai.

10. Tsabtace Kayan Shafawa da Tawul

Kayan shafa kamar brush, sponge, da tawul su kasance na mutum guda, kuma a rika wankewa akai-akai don kauce wa yaduwar kwayoyin cuta.

Karanta:

Gashi: Hanyoyi 10 na Gyara Gashi yayi Kyau yayi Sheki

WANKA A MUSULUNCI: WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA SAURANSU

Maganin da Ganyen Parsely yake da suka hada da sanayi, cancer da sauransu

Abinci Da Zai Taimaka Wajen Kula Da Fata

  • Kayan marmari kamar ayaba, abarba, apple, da watermelon
  • Kayan ganye kamar alayyahu da ugu
  • Kifi da man zaitun (omega-3 fatty acids)
  • Guji nama mai kitse da abinci mai sinadarin sukari

Lokacin Da Ya Kamata Ka Ga Likita

Idan kurajen fuska ko rashes sun ki warkewa bayan amfani da magungunan gida tsawon makonni biyu zuwa uku, ko kuma sun kara tsanani da kumburi ko zubar da pus, ya kamata a tuntubi likita ko dermatologist.

Kammalawa

Kulawa da fata na da matukar muhimmanci. Ta hanyar amfani da hanyoyin gida, kayan halitta da tsafta, zaka iya magance matsalolin fata kamar kuraje da rashes ba tare da kashe makudan kudade ko cutar da fata ba. Ka rika bin tsarin tsafta, yawan shan ruwa, da guje wa kayan da ke haddasa kuraje. Kada ka manta cewa kulawa da ciki yana da tasiri ga fatar jiki gaba ɗaya.

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari

Leave a Reply