You are currently viewing Maganin Hawan Jini:  Hanyoyi 5 Masu Amfani Domin Magance Hawan jini

Maganin Hawan Jini: Hanyoyi 5 Masu Amfani Domin Magance Hawan jini

Hawan jini cuta ce wadda take addabar mutane da yawa a fadin duniya wadda idan ta samu mutum tana da bukatar ya rika kula da karuwar ta ko kuma raguwarta a cikin jikinsa.

A cikin wannan post din inshallahu zamuyi magana akan hanyoyin da zaka bi a kimiyyance domin magance cutar hawan jini ko ince rage yawan hawan jini a jikinka.

MInene Hawan Jini

hawan jini cuta ce wadda take addabar mutane kuma yadda take shine yanayin bugawar jini ko wucewar jini a jijiyar da ake kira da arteries yake karuwa ya wuce misali wanda hakan ake cema hawan jini.

Maganin hawan jini

Yana daya daga cikin cutukan da suke kama mutane musamman ma masu kiba sosai wadda ta wuce misali wanda ciwo ne wanda yake ci ko kisa a kalkashin kasa ba tare da an ankara ba.

Illar sa idan yayi yawa yana haifar da abubuwa kamar haka

  • Bugun zuciya
  • Shanyewar rabin jiki
  • Ciwon kwada
  • Kawo matasala a idanu

na daga cikin manyan alamomin sa wanda ga duk wanda yayi masa yawa yana haddasa abubuwan da kamar yawan ciwon kai. zubar jini ta kafofin hanci da samun wahalar yin lumfashi wanda wannan alamomin suna nuna cewar a ga likita a gaggauce ba da bata lokaci ba.

Mai fama da wannan lalura ana bukatar ya rage cin abubuwan da suka shafi kitse musamman wanda baya narkewa sai kuma gishiri da kuma yawan kokarin kwantar da hankalinsa a alamuran rayuwarsa.

karanta: Addua ko Wuridin Samun Kudi

Maganin Hawan jini

Akwai hanyoyi da dama da ake bi doni rage yawan hawan jini a cikin jikin mutum kuma wanda suke kunshi tun daga kayan cin abinci. halayya dama sauransu ga kuma wasu daga cikin masu amfani sosai wanda aka dade da jarabasu a duniyar kimiyya.

Yadda ake rage hawan jini

Yawan Motsa Jiki

Motsa jiki yana da matukar amfani sosai a cikin jikin mutum kamar yadda mukayi magana rubutun da mukayi a baya, domin yana taimakawa wajen wargaza calories da sukayi yawa a cikin jikin mutum.

Yawan calories a jikin dan adam shi ke jama masa saamuwar kitse marar aamfani wanda yake haifar da toshewar kafafen gunar jini a cikin jikinsa.

To dangane da hawan jini  idan ana yawan motsa jiki koda ta yawan tafiya ne zufar da mutum yake da yawan motsa gabban sa suna taimakawa wajen narka calories da sukayi rara kuma suna taimakawa wajen rage kitse.

Karanta: Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

Bugu da kari motsa jiki yana taimakawa wajen kwantar ma mai hawan jini da jhankali musamman yadda ba’a son yana yawan tada hankalinsa.

Yayan Kabewa

yayan kabewa suna taimakawa sosai wajen rage yawan hawan da jini yayi a cikin jikin mutum musamman man su ana sun mai wannan lalurar ya dinga shan  koda kamar cokali biyu ne a duk rana akalla.

karanta: Yadda zaka magance gyanbon ciki ulcer Babba da karama

Kitsen Kifi

Kitsen kifi wanda ake kira da omega 3 kitse ne mai amfani a jikin mutum ba yada illa, kuma an son cinsa saboda amfanin da yake da shi a jiki.

To ga masu fama da lalurar yawan jini ana son su rika cinsa domin hakan yana taimakawa wajen rage hayan da yake yi kwarai da gaske.

Yawan Amfani da Tumatur

Tumatur yana daya daga cikin muhimman abubuwan da masana suka yi bincike akansa game da wannan cuta kuma suka bada tabbacin cewa yana kunshe da sinadarai masu taimakawa masu fama da wannan lalurar.

Karanta: Maganin Yawan Kasala a Jiki

Cin tumatur ko kuma yawan amfani da abubuwan da suka shafe sa yan taimakawa sosai wajen rage hawan da yayi yadda zai yi kasa inshallahu.

Karas

karas abu ne mai amfani a cikin jikin mutum wanda yake taka rawa sosai a cikin jini, yana taimakawa wajen bude kafofin jini da kuma magance wasu cututtuka dake da alaka da jini.

Mai wannan lalulura shima ana so ya yawaita amfani da karas a cikin abincinsa kai har ma haka nann kawai an son ya yawaita cinsa saboda yadda take da amfani sosai wajen karin lafiya.

 

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari