Skip to content
Home » Yadda ake Hardace Qurani

Yadda ake Hardace Qurani

Hardace Qurani abu  ce mai kyau ga rayuwar dan adam wadda ya kamata yayi saboda dimbin lada, daraja da kuma kima ga wadanda suka hardace qur’ani a duniya da kuma ranar gobe kiyama.

A yau a cikin wannan post din inshallahu zamuyi bayani akan matan da kuma abubuwan da mutum ya kamata yayi domin ya haddace qur’ani mai kirma cikin karamin lokaci kuma harda mai kyau wadda take zananna.

Hardace Qurani

Falalar hardar Qur’anin Duniya da Lahira

Hardar qurani tana da matukar amfani ga mutum musulmi a nan gidan duniya da kuma bayan ya mutu ranar alkiyamma ga kuma wasu daga cikin su kamar haka.

Ya tabbata a nassi cewa qurani zai yi ceto a ranar alkiyama ga wadanda suke ma’abota alkurani saboda yadda suka rike shi a rayuwar su ta duniya .

Abu na biyu kuma Allah yana Taimakama mutum ga duk wani karatun da ya sa a gaba, ta yadda zai ji yana sauran fahimta kuma in ya kwatanta da saurin hardar abu ba kamar wanda bai yin harda ba, a takaice dai kwakwalwa na budewa ta yadda ilimi zai rika shiga da sauri.

Amfanin hardace qur'ani

Abu na ukku kuma akwai budewar arzuki da kuma kofofin alkahi, tabbas wanda ya rike alkur’ani da gaske yana samun wannan garabasa mai tarin yawa sanadiyyar hakan mutane da yawa wadanda sukayi hardar qurani sun san haka kuma sun bada labarai da dama na irin abubuwan alkairai da suka samu.

karanta:

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

To tunda munga wasu daga cikin abubuwan falala da ake samu bari mu tafi ga yadda zaka fara hardar qurani  da abubuwan da zaka kula domin zaman hardar qur’ani mai girma.

Yadda zaka fara Hardar shi

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan kula idan kana son ka hardace kurni wanda zasu taimaka maka a wajen hardar ce shi da sauri cikin sauki.

Son Hardace shi

Kafin ka fara harda ka sani cewar ka sama ranaka kana son ka yi hardar qur’ani mai girma, kana jin shaukinsa da kuma dadin karatunsa a duka inda kaji ana yinsa.

Musamman a wannan zamani na cigaba kana iya duba gasar karatu ta zakarun duniya a YouTube wadanda suka kware ta hanyar karanta shi hakan ne zai baka himma yi sosai.

Kuma akwai wani abu duk wanda yake son abu sosai to dukan wata wahala zai iya jureta kamar yadda hausawa suke cewa sa kai wanda yafi bauta ciwo.

To ba a harda ba kawai duk wani abu mai amfani a rayuwa wanda zakai karatu ne ko kuma kasuwanci to ka sama ranka son abun zakaga ka cimma burinka inshallahu komin dadewa.

Tsarin Harda

Idan kana son kaci karfin harda to dolene ka tsara yanayin abunda zaka hardace a kullun, awata ko kuma a duk sati hakan yana tai,makawa kwarai da gaske.#

Abunda yasa shine idan baka tsara ba wata rana idan jiya ka hardace aya goma to gobe sakaci na iya hanaka ka gaza hardace biyar misali shi tsari shi ke taimakana mataki na sama wato son hardar ko kuma harzukawa.

Yadda zaka kiyaye tsarinka zaka dauka kamar alkawari ne ka daukar ma kanka wanda idan baka yi ba zaka hana kanka cin wani abinci har sai ka yi wannan abunda ka tsara zakayi.

Maimata na Baya

A wannan fanni kuma bayan ka fara hardacewa zakaga ta baya tana dan zubewa karka damu dolene ka samu hakan.

To sai ka daukin matakin yadda zaka rinka maimata ta bayan shima kadanyi tsari koda bai kai kamar yadda kake yi ba  a farkon hardar duk yadda kasa abunda ake so dai shine yin.

Ka samu cikin dare ka zabi wani yanki wanda kake tashi kana tsayuwar dare sai ka rinka maimaita ta bayan idan ka tashi domin sallar dare na kara zannan da harda da izinin Allah

Yinshi da Tajweedi

Karanta Qur’ani  ta hanyar kyautata shi dolene saboda shi ana son ka karanta shi yadda aka saukar da shi bawai yadda kaga dama ba.

Ka samu litattatafai kaje makaranta ko kuma a wajen wani malami wanda zai koya maka ilimin tajweedi wato ilimin yadda ake ba kowane harafi da kuma kalma hakkinta a cikin qur’ani.

Hakan ne zai sa ka ji karatunka yayi dadi kuma ko kaima hakan zai taimaka maka wajen jin dadin kula da karanta qur’anin a koda yaushi kamar yadda ka tsara zaka yi shi.

Kammalawa

A matsayin mutum musulmi dai ya kamata koma ince dole ne ya rike qur’ani da kyau domin shine littafinsa wanda Allah ya sauko da shi ga Annabi Muhammadu(S.A.W) zuwa ga mutane baki daya.

To hardace qur’ani kamar yadda na ambata a baya yana da falala da kuma tarin lada mai yawa a  duniya da kuma ranar Lahira.