Skip to content
Home » Yadda Zaka Duba Jarabawar Waec da Kanka

Yadda Zaka Duba Jarabawar Waec da Kanka

Sakamakon Jarabawar Waec Idan ta fito ko kai da kanka kana iya dubawa a online sai daga baya kaje computer center wajen masu sana’ar printing da photocopy su fidda ma.

Abubda ya sa nace haka shine yanayin kudin yana raguwa bisa ga ace kaje su fidda maka misali idan kana da scratch card idan zaka biya 100 to idan ka fiddo da kanaka bai fi ka biya 30 na print out ba to a cikin wannan post din zamuyi bayani dalla- dalla akna hakan inshallahu.

Bayani akan Waec

Waec ko a turance Western African Examination Council jarabawa ce wadanda yan sakandire ke yi domin samun damar shiga manyan makaratun gaba da sakandire..

Duba waec

jarabawar ba wai kawai yan Nigeri ne ke yinta ba a’a hada daliban kasar ghana, gambia, sierra leon da Gambia wanda duka suma suna zana wannan jarawar a lokacin da ake yinta.

A na son mutum ya samu akalla 5 credit wato C guda biyar amma da sharadin ya ci lissafi da kuma turanci amma amfi so ma mutum ya cinye ta da credit kuda 9 yadda duk makarantar da ya je neman admission zasu yi sautran amsar sa a matsayin dalibi.

Idan mutum yana da nakasu a daya daga cikin math wato lissafi ko English Turanci yana iaya kara zaunawa a shekara mai zuwa ya kara zanawa wato ya gyara in gyaran yayi sai ya hada su biyun yana amfani da su a matsayin cen yaci cen yana neme.

Kusan itama kamar yadda dayar jarabawar neco take wadda abaya itama munyi bayani akn yadda ake duba sakamakon Jarabawar NECO.

Hanyoyin da Zaka bi ka fiddo WAEC

To idan kana son ka duba sakamakon Jarabawar zaka shiga Internet wato yanar gizo sai ka bi wadannan matakan da zan ambata maka kamar haka.

Karanta: Yadda ake Connecting din Computer da Internet

Amma kafin nan yanzu suna bada kati ga kowane dalibi ka tabbata kana da scratch card dinka a hannunka domin shine ya kunshi bayanan da zaka rubuta ka duba sakamakon.

duba waec

  1.  zaka ziyarci shafinsuy na yanar gizo wanda shine kamar hoton da ka gani a sama- https://www.waecdirect.org/
  2. Daga nan sai ka duba katinka ka sa Lambobin jarabawar ka wato examination number
  3. Sai kuma ka zaba School Candidate ne ko private candidate
  4. sai ka rubuta pin din da ke catin
  5. Daga nan kuma sai serial Number
  6. sai ka danna Submit
  7. Bayan ka danna Sumbit sai kayi saving as pdf kaje ayi maka printing in kuma kana da printer sai ka tura mata ta fidda maka shikenan.

Karanta: Yadda ake maida page din website ya zama pdf a computer ko a waya.