Shin ko ka cewa kana gida Nigeria, Niger ko kuma cikin kaarka zaka iya zuba jari a cikin kamfunnan da ke america cikin dan karamin lokaci kuma ka samu kudi ta hanyar kason share dinka?
Wannan abun yanzu har ya fara karade duniya kuma mutane da dama suna amfani da kudinsu suna zuba ma manyan kamfannu na kasashen waje kudi wanda da share ta tashi sai kaga ka tashi da makudan kudade baka ankara ba.
Kamar yadda a baya mukayi magana akan zuba hannun jari a cikin wannan post din kuma inshallahu zamuyi bayani akan yadda abubuwan suke tafiya da kuma yadda zaka fara taka tafiyar.
Table of Contents
Saboda ni ya kamata na fara zuba Hannun Jari
Idan aka ce zuba jari ana nufin mallakar bangare na wani kamfani ta hanyar sanya kudi a cikin kamafanin wanda ake kira a turance da share.
Hakan yana ba mutum dama ta samun kudi daga kamafnin kodai ta hanayr ribar da aka samu idan an raba ko kuma za’a cigaba da shi kamfanin zai cigaba da juya maka kudin kudinka suna karuwa idan share din ta karu lokaci bayan lokaci.
A kowane hali kana iya kara mallakar bangaren hannun jarin kamfanin kuma idan kaga kana iya saidawa in kasa samu riba ko akasin haka zaka iya zare kudinka.
Kamar yadda zamani kusan yanzu ina iya cema yanayin zuba jari ya rabu ne zuwa manayan gidaje guda biyu wanda ga su kamara haka.
- Ta hanayar zubawa a cikin kasuwar cryptocurency
- Ta hanayar Stocks wato sayen bangaroren Jarin Kamfani
Karanta:
Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa
Wanda Yafi Kowa Kudi a Duniya da Tarihin yadda ya samu Kudin
Taya ake samu da shi
Yadda ake samun kudi da shi kusan abun ya rabu ne zuwa gida biyu kamar haka saboda kusan yanayin zubawar kala biyu ne akwai na digital currency akwai kuma hare system na kamfani.
A fannin digital currencies shine ya shafi zuba jari a abubuwan da suka shafi bitcoins da kuma sauran kudade na crypto wanda mutum yawanci ma da ya saya zai tsaya abun ya tasi ya saida ne kai tsaye a kasuwa kuma coin ne ka saya ba abu na kamafni ba wanada ake da shi a zahiri.
A kuma fanni na biyu shine wanda ya shafi fannin stocks na kasuwar stock exchange wanda wannan ko ina an fi yarda da shi ba kamar na coin ba shine na asalin wanda zaka iya sayen jari misali kamar a kamfanin dangote, kamafanin totyota da koma wane kanfani ka samu damar saye kuam kake da sha’a war sayen share dinsa.
Ya zan fara
Yadda zaka fara tafitar taka shine akwai applications kala kala da ake iya yin irin wannan kasuwancin amma wanda yafi kusan yanzu a nigeria aka kuma fi saninsa da yadda da shi shine chipper cash.
Applicatiuon ne wanda zaka iya downloading a playstore a Android ko a wayar Iphone kana iya samunsa sai ka bude shi kamar banki ne on ka bude.
yana da amfani sosai kuma ga wasu daga cikin abubuwan da zaka iya yi da shi kamar haka zani zayyano maka su dalla-dalla wanda zasu taimaka maka a harkokin online da kuma bankinka.
- Zuba jari na kamfunna
- Sayen Cruptocurrencu da saidashi
- Mallakar Via ta biyan kudi a gida Nigeria da KUma kasahen waje
- Tura kudi da amar kudi
- Sayen data kati da biyan bill kamar na wuta da sauransu
karanta:
Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi
Hada Game: Yadda Zaka Kirkira Game da Kanka
Author Profile
Latest entries
- Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a
- Kiwon LafiyaJanuary 3, 2025Maganin da Ganyen Parsely yake da suka hada da sanayi, cancer da sauransu
- KasuwanciJanuary 1, 2025Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa
- Sana'o'iJanuary 1, 2025Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya
Inason inyi kasuwanci
Ok ciki wane make son farawa