Skip to content
Home » Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa

Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa

Kudi abu ne wanda idan mutum yana da su akwai bukatar ya tsaya a mafi yawancin lokutta yayi tunanin wane irin kasuwanci zai yi da su. Domin ba kawai haka nan take wani lokacin mutum zai zabi abunda zai yi da su ba sai ya tsaya ya yayi tunani.

zuba jari a hanyoyin da suke rub awa

Hanyoyin Juya Kudi masu Matukar Riba

Su kudi mutane suna yin kuskure sai su kai su banki su aje hakanan, amadadin kayi wani abunb da su sai mutum ya taskace su yadda basu karuwa kuma suma inda ka kai bankin juya su zasuyi kuma basu baka wani abu tun ba zuba hannun jari kayi ba, shiyasa masane ke cewa mai wayau shi ke juya kudi ba ajiya ba.

To inshallahu a cikin wannan post zamu yi magana wasu muhimman bangarin da mafi akasari musamman a duniyar yanzu idan aka zuba masu jari ana yawan samun riba, ma’ana akwai karancin asara a tattare da irin wadannan kasuwancin. kuma gasu daya bayan daya tare da bayaninsu.

Kaddarar Gidaje da Filaye

Sayen kadara da sayarwa sana’a ce kuma jari ne babba da zaka zabar ma kanka,  wadda bata da faduwa sosai gaskiya kuma mafi yawanci ma riba ake ci indai ba ace abun ya lalce ba ko kuma ya kone wanda wannan daman asara ce ta gama gari kowa tana iya hawansa.

Kaddara abunda ya shafi filaye da gidaje mallakarsu ba karamin abu bane kuma yana da matukar ribar gaske saboda misali yanzu mutum idan ya sayi fili bayan shekara ukku filin nan ya kara ya bar farashin da ya saya unguwa ta kara daraja kila ya rua kudin da ya saya.

sayen gida da saidawa

Haka kuma balle a ce gida, mallakar gida ba karamin abu bane saboda mutum koba shi yake zaune ba yana sa yan haya banda ace kila akwai shagon da yake tare da shi wan da za’a cigaba da kawo masa kudi a duk shekara.

Karamin misalin ribar abun yadda zata fito ma shine misali ka maallaki gida shida koda baka aiki suna iya isar mutum mai matasakaicin kashe kudi.

kamar ace hayar kowane ya kamar N130,000 ba wani babban gida bane a manyan birane idan ka yi sau 6 zai kama N780,000 duka idan ka raba sau sha biyu N65, 000 a duk shekara kowane wata.

To wannan a fannin haya kenan kawai banda in kagadamar sayar da gidan zaka samu riba.

Kiwon Dabbobi Manya

Kiwo dai musamman a zamani yanzu an yi walkiya kowa ya gani yadda rago yake kai kudi sosai kamar za’a sayi sa da kudinsa.

Mutane masu wayau suna samun dabbobi da kudinsu amadadin su aje su a banki su fara sana’ar kiwo da su wanda cikin shekara musamman ma a ce lokacin sallah babba ya taho lokacin da mutane ke neman dabbobin da zasu yi layya suna yin tsada sosai.

To kiwo duk da dukansu suna da riba dana kajin dana dabbobin duka amma gaskiya kusan na dabbobi da kuma shanu yanzu kusan yafi riba musamman yadda yanayin masu kiwon suka ragu a kauyuka da kuma yadda neman dabbobin yake kara yawa koina.

Karanta:

Sana’ar Kiwon Kaji da yadda ake samun kudi da ita

Sana’ar Kiwon Kaji da yadda ake samun kudi da ita

Abubuwan Sufuri

Sayen abubuwan sufuri kamar su mota, adaidaita, mashin kai harma da keke da sayar da su hanya ce babba itama da take ruba jarin da mutum yake da shi ya zuba a kasuwancin saboda kusan kullun kara tashi sukeyi kuma kara neman su ake.

sana'ar saida motoci

saboda musamman idan mutum ya sayi mota ya kawo ta second daga wata kasa zuwa wata kasa shifa irin wannan kasuwancin a basu ci riba ba shine su tashi da N50,000 wanda fiye da haka ma ake samua a fannin.

Kuma fannin wannan sana’ar duka ya shafi second ne ko sabo wani lokacin sayen sabon yafi riba a saida wani kuma lokacin secon din ne mutum yake saye sai ya saida ya samu riba mai yawa baya ya yi masa gyara idan da yana da matsala.

Karanta: 

Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Mallakar Share

Mallakar share ba wani abu bane illa zuba hannun jari ga kamfunna da suke bunkasa, zuba ma irin wadannan kamfunna jari yana kwau sosai saboda da sun mike kaima kason da ka zuba zai kari.

Kuma wasu ma daga cikin irin wadannan kamfunnan suna bada abunda ake cema cdevident wato kason ribar da kamfani ya samu  kamar yadda mukayibayani akan zuba hannun jari amfaninsa da kuma abubuwan da suka shafe shi

Karanta :

Samun kudi ta Zuba Hannun Jari

Noma

Abu na gaba kuma shine noma baubuwa  da ya shafi noma, daman arziki yana cikin noma ba wai  acikin petur ko wani abun  ma’adani ba.

Domin duk kasar da bata iya noma abinda zata iya cida yan kasatrta komin arzikinta zakaga yana tafiya a kan abinci ne , to shi noma ya kasu kashi biyu akwai na abinci akwai kuma na lambu koma kowane da fa’idarsa.

Amma wani lokacin na lambun ya fi musamman idan ya habbaka ba’a yi masa aiki sosai kamar yadda gonar abincin da ake da ke ci wato tsaba ake ywan yimai kuma yanayin riba tafi rubawa.

Dalili kuwa shine ydda wasu itatuwan sun riga da girma ba sai ka basu ruwa ba kawai sai adai  ka kula da su duk shekara ka rika saida ma masu sari.

Karanta: 

Yadda ake hada man shafawa verseline

Manyan Sanaoin Gargajiya na Kasar Hausa wanda Hausawa Ke yi