Skip to content
Home » Yadda ake Farsfesun Nama

Yadda ake Farsfesun Nama

Farfesun Nama

Yadda ake Farsfesun Nama

 Assalamu Alaikum barka da ziyarto wannan shafi maialbarka, kamar yadda aka saba har kullun yau post din namu  munzo ne akan yadda ake farfesu na nama wato (pepper souf) a turance wanda inshallah zani yi maku bayani gamsasshe akan yadda ake hada si.

To indai ba’a manta ta a bayanin a wannan website mai albarka wato Hausawa Site mun yi post akan yadda ake hada Cin-Cin, Cake, Fanke, Fried Rice da ma sauran nauka na girki kala-kala.

To bari mu fara lissafa kayan hadin da ake bukata wajen farfesu gasu kamar haka:

Nama

Kayan da Ake Bukata wajen Hadawa

Gasu Kamar Haka

  1. Nama
  2. Gishiri
  3. Man Gyada
  4. Thyme
  5. Kori
  6. Man ja
  7. Kayanj miya
  8. Ruwa
Karanta: 

Yadda Ake Hadawa

Kayan da muka ambata a sama sune ake Bukata ga kuma yadda ake hada su su bada farfesu:
Da farko dai Idan kida yanka Namanki, sai ki sai ki dauraye shi ki rufe a gefe guda, sannan sai ki markade cefanenki ki hada da su citta, tafarnuwa da karamfani.
Dauko Naman da kika aje a dazu ki dora shi a saman tukunya ki dan sulalashi  ko ki dafa shi, bayan ya dafu sai ki safke ki rufe shia gefe guda.
Daga nan kuma sai ki daura tukunya ki zuba mai da mai ki soya markadadden cefanenki, sai ki zuba ruwa ki motsa bayan nan kuma sai ki kawo maggi, gishiri ki zuba ki motsa su sai ki kulle ta dahu.
Daga nan kuma sai ki dauko wannan naman ki zuba bayan kin bashi mintunasai ki dauko thyme, kori citta da tafarnuwa,da karanfani wadanda aka daka sai ki zuba a cikin tukunyar,
Daga nan sai ki cigaba da motsasu saboda kar yayi kamu sai bashi mintuna shikenan sai ki samu kula ki zuba a ciki.