Skip to content
Home » Manhajar software da ya kamata ka zaba domin Kasuwanci

Manhajar software da ya kamata ka zaba domin Kasuwanci

Idan mukayi magana akan inganta kasuwanci a yanzu tabbas abubuwa da dama sun sauwa sanadiyyar cigaban kimiyya da fasaha wanda ya kunshi na yanar gizo Internet da makamantansu wanda suke taimakama dan kasuwa.

A cikin wannan rubutun inshallahu zamu yi magana akan wasu muhimman abubuwan da zasu taimaka maka wajen zabar manhaja imma ta wayar hannu, wadda take aiki a computer ko kuma wadda a Internet ne kawai ma ake samunta.

Amma kafin nan bari muyi matshiya akan wasu muhimman abubuwan da ya kamat ka fara fahimta da farko.

naukan manhaja domin kasuwanci

Mi ake nufi da manhajar kasuwanci?

Idan akayi magana akan wannan batun ana nufin yin amfani da aikace aikacen naura mai kwakwalewa na cikinta domin habbaka kasuwanci.

Kmar dai yadda ma’anar software take abu ne wannda ba’a gani a fili sai cikin computer amma zaka iya amgfani da shi ya gudanar maka da wani aiki.

To a nan muna magana ne a fannin kasuwanci ina nufin wadda take amfanarwa a fannin kasuwa ba wani fanni na daban ba kuma.

da farko dai ya kamata ka sani a kayan aikin da muke amfani da su na na’ura aikin manhaja ya rabu zuwa gida ukku kamara haka.

  • Manhajar da ke aiki a wayar hannu ko kananun na;ura
  • Manhajar da ke aiki a computer
  • Manhajar Online

Karanta :Yadda ake hada Android Application

Rabuwar su a fannin kudi

A kuma yanayin kudi ko ace farashi yadda zakayi aiki da su sun rabu gidaje kamar haka, wanda kafin kayi amfani da wata yana kyau ka fara fahimtar wannan bayanin.

Ta kyauta free

Software ta kyauta a turance ana kiranta da free software wadda manhaja ce wadda kamfanin da yayita suka kirkira ta a matsayin mutane suyi aiki da ita kyauta babu wata bukatar su b iya kudi zasi iya sauke ta.

Irin wadannan manhajojin yana wani lokacin kamfanonin da suka hada su suna samun kudin shiga ne ta hanyar tallafawa ko kuma ta hanyar kara ma software wani abu ta bayan fage wadda zai kara mata aikace aikace.

Ya danganta suna iya cewa su kadai zasu hada abun karin aikin ko kuma sunba hada sauran mutane damar yin hakan.

Ta saye lokaci daya

Ta biyu kuma ita ce wadda ta saye ce sai ka biya kudi za’a baka kayi amfani da ita a kasuwancinka ko kuma wani abunda kake son kayi da ita.

Irin wannan manhaja ita kuma yadda kamfanonin da suka yi ta suke samun kudaden shiga shine ta hanyar sayar da ita.

Ya danganta suna iya cewa baka iya download kayi install din software dinsu sai ka biya ko kuma su baka wasu yan kwanakin da zaka dan tosa ka jaraba su rike kayansu

Ta Biya bayan lokaci lokaci

Ita kuma ta gaba ita ce wadda ake biya bayan lokaci lokaci ko kuma zango bayan zango ya danganta wadda ake kira da subscription based a turance.

Ita wannan kawai zaka cigaba da biya da zaran ka bari to zasu hana ka aiki da abunsu in ka dawo ka cigaba da aiki da ita wannan yawancin manhajojin online dsunfi amafani da tsari.

Kuma mafi akasari zakaga irin wannan manhaja tana da inganci da kuma aiki yadda ya kamata sosai.

To bayan haka abu na gaba sai mu tafi akan muhimman abububuwan da ya kamata ka kula da su idan kana son zaba ta kasuwancin da kake yi.

muhimman abubuwan kulawa a kasuwa

Yadda zaka zabi wadda zatayi maka

Ita hnayar samu ba abun wasa ba ce  kafin ka zabi wadda taka yana da kyau ka kula domin kada gaba wata ,matsala ta kunno kai wadda babu mai son hakan.

Ga kuma wasu daga cikin muhimman abubuwan da zaka kula da su kamar haka zan lissafa su.

  • Wane irin aiki zakayi da ita
  • Idan ka sameta ka duba kamfanin yana update dinta yana kyara ta lokaci bayan lokaci
  • Shin suna bada support wani taimako koda ka shiga wata matsala gaba
  • Ya customin ka zasu ji abun zai kyara masu ko kuma zai basu matsala
  • Kai kana iya amfani da ita kana samun saukin aiki da ita koko
  • Shin tana da lafiya ba tada illar virus in kuma ya kama ta akwai magani anti virus koko.

Abubuwan da muka zayyana a sama sune abun lura don haka sai a kula a cigaba da kasancewa da mu ia  WWW.HAUSAWASITE.COM.NG a koda yaushe.

Karanta :

Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

Yadda zaka samu subscribers Masu Yawa a YouTube Channel

Blog da Abubuwan da ya Kunsa