Skip to content
Home » Saida Waya: Bayani akan Yadda zaka fara saye da saida waya(handset)

Saida Waya: Bayani akan Yadda zaka fara saye da saida waya(handset)

Saida wayoyin hannu sana’a ce ko kuma ince kasuwanci ne mai matukar amfani, kuma ana samun kudi da shi sosai saboda yadda yanzu kusan kowanene kaga bashi da waya babba to gaskiya bai samu yadda yake so ba.

Musamman manyan wayoyi na yanzu wanda ake tashensu wanda suka kunshi Andoid dama babbar takwarar ta wadda ita ce iphone kowa guin shi ya samu babba to kaga wannan dama ce.

Kasuwancin saida waya

A dalilin haka ne a yau inshallahu zamuyi dubi akan yanayin kasuwancinta, yadda take da kuma yadda take saurin canzawa tare da bayani kadan akan yanayin da ya kamata kayi taka tsantan da shi.

Ya Kasuwancin Waya Yake?

Wannan kasuwanci na waya yana daga cikin nauikan kasuwanci na communication wanda muka yi magana akan shi a baya, wanda bangare ne babba a cikin wannan harkar kuma wanda ake samu da shi sosai.

shi dai waannan kasuwancin yana da bukatar zari  koda a ce ba wai babba ba amma mai dan karfi duk da dai ya danganta da shin sababbi ne zaka rika saidawa koko second wanda ake saye daga masu amfani fda ata a saida ma mai saye.

kafin ka fara yana da bukatar kasan wayoyi kirar kamfani kala daban daban da kuma sanin yadda yanayin gfarashinsu yake  sai dai a yanayin kasuwar taka zata fada ne cikin biyu daya daga cikin abubuwan da zan yi bayani akan su.

saida waya

Kasuwanci Sababbi

saida sababbin wayoyi abu ne mai kyau kuma wanda ake cin riba akanshi amma fa akwai abun lura game da shi shine yanzu musamman tunda yawancin kamfunna na kasar china ne na waya Android suna saurin fidda waya sabuwa.

kana sawo wancen version din kana iya ganin ba’a shekara sai kaga ambar yayinta sunyi ta gaba da ita kaga akwai matsala shiyasa sai kayi taka tsantsan.

Idan ba haka ba saurin faduwa na zuwa udan aka samu jinkirin kasuwa, shiyasa indai irin na sabbi zakayi to ka tabbatar ka tanadi yanayin da customer zai zo ya saye maka da wuri.

Kuma ka tabbatar dama da sauki ka sawo kuma da sauki zaka saida saboda sannar kasuwa ce ana sanin yanayin kimar waya idan ana yayinta kuma ka tabbatar kana sawo wadanda ake yayinsu ba wanda aka bar yayinsu ba.

Karanta: Muhimman Abubuwan da suke Taimakawa wajen samun Nasara a Kasuwanci

Kasuwancin Second

Fanni na biyu kuma a cikin Kasuwancin saida waya shine masu sana’ar saida second,wanda shine yawancin mutane suke yi musamman masu saida kayan communication.

Saida secon gaskiya akwai bukatar ace ka san waya sosai idan son samu mai akai a ce ka iya gyaran waya domin  idan ka iya gyara ta dama ka santa kuma hakan zai baka damar rage kashe ma mai matsala kudi idan a ce misalai ba kai zaka gyara ba.

kaga riba zata ragu, amma idan ka iya sai ka gyara ka samata cover mai kyau in tata ta lalace ka sa screen guard da sauran abubuwan da zai ja hanakalin mai saye.

Karanta:

Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya

Sana’ar Bookshop Littafai da yadda ake fara ta

Abubuwan da ya kamata Ka kula da su

Musamman ga wanda shi harkar secon din waya yake tofa sai ya kula saboda ana iya kawo masa waya ta sata a ce ya saya yaga sauki kawai ya saya wanda idan asirin wancen ya tonu kana iya tsintar kanka a ploice station fannin sata kenan.

sai kuma akwai fannin laifi wani na iya yin wani mugin abu da wayar ya nemi saida kaga nan ma akwai matsala, shiyasa yana da kayau wanda ya kawo maka abun saidawa ka yi masa tambaya sosai idan baka yadda da shi ba ka bar masa abunsa.