Skip to content
Home » Adashe: Sana’ar Adashe da yadda ake yinta

Adashe: Sana’ar Adashe da yadda ake yinta

Adashe dai kamar yadda aka sani ya zama ruwan dare, don yanzu ko ina ana yinsa kuma akwai mutane da yawa wanda suka dauki sana’ar adashe a matsyin hanyar da suke samun kudi. to sai dai menene adashe kuma ya ake sana’ar adashe irerensa nawa ne?

Minene Adashi?

Idan aka ce adashi ana nufin adana kudi ko juya su ta wani fasalin ta hanyar yadda za’a same su gaba. Babbab amfanin adashe shine ayi ajiya domin amfanin gaba wanda dole saida adanawa ake samu.

Saboda su kudi a koda yaushe idan ba’a yimasu tsari ba idan mutum yana samunsu kadan kadan yana kashewa, amma idan yayi wani tsari na adanawa zai rage kashe su wanda a gaba hakan zai bashi damar yin amfani da su yayi wani abu babba da su.

A hausa an dade ana yin adashe kuma shi wanda yake shugaban adashen ana kiransa da uban adashe, wanda shine yake tattara kudin kowane daya daga cikin mutanen da suka shiga wannan tsarin.

Karanta: Hanyoyin Zamani da ake bi Domin Samun Customers Masu Yawa

Ire-Irensa

Adashe ya rabu kusan gida ukku akasarin yadda aka sansa, koma kowane daya daga cikinsu da yadda ake yinsa da kuma yanayin mutanen da suka fi yawan yinsa duk da dai ganin dama ce kowane iri kana iya dauka kayi.

Adashen Gata

Adashen gatayana daya daga cikin ire-iren adashe wanda ake yi kuma mafi yawanci mata sunfi yinsa.

Yadda yake shine uban adashe zai samo mutanen da yake ganin zasu iya zuba kudi a yanayin yadda suka tsara sati sati ko rana rana ko wata wata.

A yanayin yadda aka tsara ana son kowane idan lokacin da aka kayyade yayi wani abu zai saya dama za’a zo da abubuwa aceka zuba idan lokaci kaza yayi za’a baka takalmi na kaza misali.

Adashen Kwasa

Adashen kwasa shi kuma yadda yake shine za’a yi tsari kan yadda za’a rika kwasar kudaden da aka zuba rana rana ko sati sati ko kuma wata wata.

Misali idana kullun ana zuba naira dubu daya aka ce a cikin kwana goma ana son wanda zai kwasa ya kwashi dubu goma.

Dama a farko uban adashe yayi tsari ya ba kowa kwasa daga ta daya zuwa ta goma misali kuma kowanensu yana kokarin zubawa duk bayan kwana goma din nan domin aba dan uwansa.

Karanta: Sanaoin Mata wanda zasu iya yi a Gida domin su samu kudi

Adashen Ajiya

Sai kuma wanda ake kira da adashen Ajiya shi ma yana daga cikin irinsu wanda shi kuma tsarinsa na daban ne kawai zubawa za’a yi tayi uban adashe yana amsa.

Shi misalinsa kamar na ajiya ne kawai rana daya uban adshe zai ware wadda kowa zai amshi kudinsa da tayi ya ba kowa.

Shi wannan baya da bambanci da yanayin ajiya a banki sosai kawai ajiyar kudice kamar yadda kowa ya sani domin amfanin gaba.

Karanta: Fasahar Kirar Zamani ta 3d Printing da Yadda Take

Ya Uban Adashe yake Samu?

Uban adashe shine yake aikin tsarawa da kuma lura da yadda kowa yake zubi da kuma bada kwasa wanda shine babba a wannan fanin.

A dalilin aikin da yake yi yana sanar da wadanda yake ma aikin cewa zasu biyashi wani kaso daga cikin kwasar kowa ko kuma idan kowa ya kwasa.

Suna ware wani kaso ne wanda shi ake kira da gurbi a hausance to mafi yawanci wannan ce hanyar da uban adashe yake samu da ita.

Sai kuma misali hanya ta biyu a fannin adashen gata yana iya saida hajar da mai zubi za’a bashi ita.

Karanta: 

Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi

Sana’oin Zamani 10 Masu Saukin Yi ga Mazauna Kauye ko Karkara

Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa

Sana’ar POS da yadda ake yinta